CORONAVIRUS: Kogi ta umurci kashi 70 bisa 100 na ma’aikatan jihar su zauna a gida

0

Gwamnatin jihar Kogi ta umurci ma’aikatanta daga maraki 1 zuwa 13 su zauna a gida na tsawon kwanaki 14 domin hana yaduwar cutar coronavirus a jihar.

Kwamishinan yada labarai Kingsley Fanwo ya sanar da haka yana mai cewa ma’aikata za su fara aiki daga gidajen su ranar Litini 23 ga watan Maris.

Fanwo yace wadannan rukunin ma’aikata da za su zauna a gida sun kai kashi 70 bisa 100 na ma’aikatan jihar.

Yace jami’an kula da lafiya, ma’aikatan kwashe shara, jami’an kashe gobara da sauran masu ayyukan agajin gaggawa ba za su zauna a gida ba.

Har yansu dai babu wanda ya kamu da cutar a jihar amma gwamnati ta ce tana kokarin ganin cutar bata shigo shigo jihar ba.

Idan ba a manta ba gwamnatin Jihar Legas ta umarci kashi 70% bisa 100% na ma’aikatan jihar da kada su fitar aiki, har tsawon kwanaki 14, tun daga ranar Litinin, 23 Ga Maris.

Wannan umarni ya shafi dukkan ma’aikatan jihar masu matakin albashi daga Level 1 zuwa Level 12, wadanda sun kunshi kashi 70% bisa 100% na ilahirin ma’aikatan gwamnatin jihar Lagos

Gwamnati ta dauki wannan matakin gaggawa ne, ganin yadda cutar Coronavirus ke kara ci gaba yaduwa a Lagos.

A yanzu dai mutane 32 ne ke dauke da cutar,biyu sun warke sannan daya ya mutu a Najeriya.

Sannan daga cikin mutane 32 din da suka kamu da cutar 19 a jihar Legas suke.

Haka ita ma jihar Kwara da Kaduna, duk sun bi sawu. Gundumomin babban birnin tarayya ma sun saka irin wannan dokar.

Share.

game da Author