DAMBARWAR ZABEN IMO: Ihedioha ya roki kotu ta kara masa lokacin gabatar da hujjoji

0

Tsigaggen gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, ya roki Kotun Kotu ta kara masa wa’adin karin lokaci ko da na kwanaki 7 ne domin ya gabatar da hujjojin cewa shi ne ya ci zabe, ba Hope Uzodinma da kotun ta kwace ta baiwa ba.

Ihedioha shi da jam’iyyar PDP sun gabatar da wannan bukata ce a zaman Kotun Koli na Talata, domin sake bin ba’asi da katin shari’ar farko da kotun ta yanke, wadda Ihedioha ya ce damfara ce aka yi masa, aka kwace kujerar gwamna a hannun sa, aka bai wa wanda ya zo na hudu.

Ya yi wannan roko ne ta hannun lauyan sa Kanu Igabi, wanda bayan ya gabatar wa kotu wannan roko, sauran lauyoyin wanda ake kara, wato APC da Hope Uzodinma, ba su yi jayayya ba, suka amince a kara masa lokacin.

Alkalan kotun su 7 bisa jagorancin Cif Jojin Najeriya, Tanko Muhammed, sun amince da rokon da ya yi, kuma suka kaga sauraren karar zuwa ranar 2 Ga Maris.

Emeka Ihedioha, wanda ya yi nasara a ranar 9 Ga Maris, 2019, kuma aka rantsar da shi, an tsige shi, aka dora Hope Uzodinma na APC.

Ihedioha ya sake garzayawa kotu, inda ya yi zargin cewa an kayar da shi a shari’a mai cike da daurin-gwarmai da harkalla, inda aka tsige shi aka dora wanda ya zo na hudu a zaben.

Ya sake shigar da sabuwar kara a ranar 5 Ga Fabrairu a Kotun Koli, bayan an yi ta korafe-korafen cewa an tabka makarkashiya a hukuncin da Kotun Koli din ta yance ido-rufe.

A hukuncin da Kotun Koli ta yanke, a karkashin jagorancin Babbar Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta ce an cire sakamakon zaben rumfuna 388 ba bisa ka’ida ba.

Ta kwaso sakamakon da ta ce shi ne na rumfunan 388, inda ta ce Uzodinma ne ya lashe zaben idan aka hada masa da adadin kuri’un sa da ya zo na hudu da su.

Alamomin Tambaya

Kotun Koli ta bar kofar fitowa karara ana zargi, yayin da ta ki fito da sakamakon da kowace jam’iyya ta samu a wannan rumfuna 388 sai na APC kadai.

Daga nan sai Kotun Koli ta umarci INEC ta kace satifiket na shaidar lashe zabe daga Ihedioha na PDP, ta damka sabo ga Uzodinma na APC.

Sai dai shi kuma Uzodinma ya ce tunda kwanaki 60 da doka ta ce a cikin su ne za a iya daukaka kara sun wuce, to bai ga dalilin da zai sa a sake tusa wannan shari’a ba.

Lauyoyin Uzordinma sun ce Kotun Koli ba za ta taba zama mai sauraren daukaka karar da ta rigaya ta yanke ba.

Sun kara da cewa Kotun Koli ta haramta wa kanta sake bin kadin wata shari’a da ta rigaya ta yanke, in dai ba gyara za ta yi a kan kura-kuran rubutu ko wata subul-da-baka ba.

Sai dai kuma a ranar 18 Ga Fabrairu ne Kotun Koli za ta zauna ta bayyana shin za ta iya sauraren karar da Ihedioha ya sake shigarwa ko kuwa ba za ta iya ba.

Ita dai INEC ta ce ta na nan a kan matsayin ta cewa Ihedioha na PDP ne ya lashe zaben, ba Uzodinma na APC da Kotun Koli ta bai wa kujerar ba.

Share.

game da Author