Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya hana bara na yara Almajirai kwata-kwata a fadin jihar.
Kakakin gwamna Ganduje, Abba Anwar ya bayyana haka a takarda da ya aika wa PREMIUM TIMES ranar Talata.
Anwar yace gwamnati ta yi haka ne domin samun nasarar shirin bada ilimin Firamare da Sakandare kyauta a fadin jihar.
Sannan kuma gwamnati ta shirya wani tsari da zai inganta makarantun Almajirai, sannan kuma dole malaman dake karantar da yaran su bi umarnin gwamnati su tabbata sun hana yara barace-barace a jihar.
“ Duk malamin Almajiran da bai amince da wannan doka ta gwamnati ba toh ya tattara ya fice daga jihar Kano.”
“ Duk Almajirin da aka kama ya na bara, to ba Almajirin za a kama ba, za a je a taso keyar mahaifinsa ko kuma wanda yake zama wurin sa zuwa kotu domin a hukunta su.”
Gwamna Ganduje ya bayyana wannan doka ce a wajen taron kaddamarwa da mika wa malamai 7,500 takardar samun aikin sakai a jihar.
“ Shirin bada ilimin Firamare da Sakandare kyauta kuma dole ga yara a jihar zai yi nasara ne a dalilin garwaya shi da tsarin karatun Almajirai. A dalilin haka za a rika karantar da Turanci da Lissafi a makarantun Almajira.” Inji Ganduje.
Kamar yadda ya fadi, yaran za su ci gaba da karatun su na addini sannan a na koya musu Turanci da lissafi.
“ Hakan zai sa ko bayan sun kamala za su iya ci gaba da karatun su na sakandare, har ma fiye.”
Discussion about this post