Rundunar Bataliyar Sojoji ta 232 ta ce sojojin ta na Burged ta 23 da ke yakin ‘Operation Lafiya Dole’, wadanda aka girke a Gombi, sun tarwatsa gungun Boko Haram da suka yi kokarin kai hari a garin Garkida, Karamar Hukumar Gombi, cikin Jihar Adamawa.
Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Runduna ta 23, Haruna Sani ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Sai dai kuma a cikin sanarwar ya ce maharan sun dira a wani gari, inda suka rika banka wa gine-gine wuta kuma su na harbe-harbe.
Ya ce daga nan fa sojoji suka tunkare su aka rika bude musu wuta.
Ya ce maharan sun isa garin a cikin motocin harba manyan bindigogi da kuma wasu a kan babura.
Ya ce an kashe Boko Haram da dama, wasu kuma an ji musu raunuka,. Daga nan suka tarwatse, suka tsere, yawanci da raunuka a jikin su, kamar yadda aka rika ganin zubar jini a hanyar da suka bi suka arce.
Amma kuma ya ce soja daya ya rasa ran sa, daya kuma an ji masa ciwo.
Ya ce Kwamandan Burget ta 23, Sani Mohammed ya ziyarci garin na Garkida, kuma ya je ya ga irin abin da iya faru a garin.
Kwamandan ya jinjina wa sojoji da jama’ar garin.
Yadda Rahotanni Suka Bayyana Barnar Boko Haram a Garkida
Rahotanni daga wasu kafafen yada labarai sun ruwaito cewa Boko Haram sun kone barikin ‘yan sanda, Ofishin ‘Yan Sanda coci-coci guda biyu da kuma gidan wani tsohon Janar na mai ritaya, wato Paul Tarfa.
Kungiyar ta’addancin ISWAP ta ce ita ce ta kai harin. Ta kara da cewa ta kashe soja uku, ta arce da wasu masu bauta da ta ritsa a cikin coci.
Coci-cocin da aka kone sun hada da Living Faith da kuma EYN. Sun nuna cewa sun yi awon gaba da wasu mutane da suka kama a kauyukan da suka keta.
Garkida na yankin Gombi kan hanyar Gombi zuwa Biyu zuwa Damaturu.