NAZARI: DA SAURAN KALLO: Hujjoji 15 da Maryam Sanda ke kalubalantar hukuncin rataya a Kotun Daukaka Kara

0

Cikin wannan mako ne Maryam Sanda ta daukaka karar hukuncin kisa ta hanyar rataya da Mai Shari’a Yusuf Halilu na Babbar Kotun Abuja ya yanke mata a ranar 27 Ga Janairu, 2020.

An yanke mata hukuncin ne saboda Mai Shari’a ya ce ya same ta da lain kashe mijin ta Bilyaminu Halliru da wuka cikin watan Nuwamba, 2017.

A wannan kara da Maryam ta daukaka, ko shakka babu za a sa ido sosai a ga yadda za ta kaya a kotu, saboda ko ba komai, ita Kotun Daukaka Kara za ta tsaya a tsanake ta duba shari’ar baya da Halilu ya yanke, tare da duba hujjojin da ya yi amfani da su.

Sannan kuma za a bi matakan kare kan ta da Maryam da ta gabatar yanzu a ita Kotun Daukaka Karar.

Tabbas Maryam ta tashi tsaye wajen kokarin ceton ran ta a wannan kara da ta daukaka, idan aka yi la’akari da yadda ta dauki babban lauya, Ricky Tarfa a matsayin babban lauyan da zai kare ta.

Wurare 15 Da Maryam Sanda Ke Kalubalantar Hukuncin Rataye Ta

1. Maryam ta ce ba ita ta kashe mijin ta Bilyaminu ba, amma Mai Shari’a Halilu ya yi amfani da hujjoji na badini, ba zahiri ba, ya yi mata hukunci.

2. Ta ce Mai Shari’a bai tsaya tsaf ya dora hujjojin da shaidu suka gabatar masa a kan doron da zai yi wa ita Maryam din adalci ba. Ta ce ya nuna son kai, ko son ran sa.

3. Maryam ta ce dukkan shaidun da suka yi wa kotu bayani, babu wanda yace an yi kisan a gaban idon sa, ko kuma ya ga lokacin da Maryam ta kashe Bilyaminu.

4. Har aka fara shari’ar aka kammala, tsawon shekaru biyu, ba a gabatar wa kotu da wukar da aka ce ita Maryam din ta kashe mijin ta Bilyaminu da ita ba.

5. Ba a gabatar wa kotu da sakamakon bincike daga likitoci da ya tabbatar musabbabin mutuwar Bilyaminu ba.

6. Lauyan Maryam, wato sanannen lauya Rickey Tarfa, ya ce Mai Shari’a Yusuf Halilu ya yi kasassaba a ranar da ya yanke hukunci, inda ya ce ya gano shaidar Maryam ce ta yi kisan a kan wani bincike da ya yi.

“Ina so na bayyana cewa akwai nauyin da ya rataya a wuya na, wato yin bincike da kuma gano abin da zai gamsar da shari’a domin yin hukunci mai adalci.”

7. Rickey Tarfa ya ce babu inda a doka aka ce Mai Shari’a ya fita wajen kotu neman wata ko wasu shaidun da zai kama wanda ake zargi da laifi.

8. Ya ce alkali na amfani ne kawai da shaidar da ’yan sanda suka gabatar masa, ko kuma furucin wasu shaidun da su ‘yan sandan ne suka gabatar masa da su a kotu.

9. Ya ce Mai Shari’a Yusuf Halilu ya nuna shi ne mai gabatar da kara, mai bincike, kuma mai yanke hukunci, duk shi kadai. Wannan inji Tarfa, babban kuskure ne alkalin ya tafka.

10. Mai shari’a ya ki tsayawa a kan hujjojin da dan sanda mai gabatar da kara ya gabatar masa, sai ya tafi kallar wasu hujjojin da babu su a cikin tulin hujjojin dan sanda mai gabatar da kasa.

11. Hujjar da mai shari’a ya kara kafawa wadda wani mai gabatar da shaida ya ce Maryam Sanda ce ta karshe da aka ga mamacin da ita kafin mutuwar sa, ba hujja ba ce wannan.

12. Lauya ya ce don kai ne na karshen ganin mutum kafin mutuwar sa ko kashe shi, ai ba lallai ne a ce kai ne ajalin sa ba.

13. Lauya ya ce ba ma ita Maryam din ba ce ta karshen ganin Bilyaminu kafin mutuwar sa, domin shi wanda ya gabatar da wannan shaida, ya bayyana wa Mai Shari’a cewa mamacin ne da kan sa ya kira shi. Da ya je kuma ya tambaye shi mene ne matsalar.

14. Lauyan Maryam ya ce bayanan da Sadiya Aminu ta yi wa Mai Shari’a sun tabbatar da cewa lokacin da ta je ta ga Bilyaminu, da ran ta ta same shi da rauni a jikin sa, ba a mace ba.

15. “Hujjar badini wadda alkali ya yi amfani da ita cewa Maryam ce ta karshen ganin Bilyaminu, ba ta tabbatar zahiri muraran cewa Maryam din ce ta kashe shi ba.

Share.

game da Author