Sanatoci sun yi watsi da muradin neman kafa hukumar saisaita rayuwar tubabbun ‘yan Boko Haram

0

Wasu sanatoci sun yi tofin Allah-wadai tare da nuna rashin amincewar su da wani kudiri, wanda wani sanata ya gabatar, inda ya nemi a kafa hukumar saisaita rayuwar tubabbun Boko Haram.

Sun ce wannan kudiri da wannan sanata ya gabatar a Majalisar Dattawa, soki-burutsu ne kawai, asarar kudi ne kawai za a yi, sannan kuwa bai ma dace ba.

Baya ga wannan, sanatocin sun ce su na tababa da kokwanton cewa yawancin ‘yan Boko Haram din, ba ma ‘yan Najeriya ba ne.

Sanata Ibrahim Geidam daga Jihar Yobe ne ya bijiro da muradin kudirin a daidai lokacin da ake caccakar gwamnatin tarayya a shirin da ta ke ta yi na gyaran halaye da dabi’un wadanda ta kira ‘tubabbun ‘yan Boko Haram.’

An ce ana koya wa tubabbun karatun zamani, na addinin Musulunci, sana’o’in hannu da kuma hanyoyin saisaita musu tunani daga dankwafar da kwakwalwa sanadiyyar shaye-,shayen kwayoyi.

Cikin shekarar da ta gabata, wasu dattawan Barno a karkashin jagorancin tsohon gwamna Kashim Shettima, sun shaida rashin amicewar su da wannan shirin, wanda suka ce sojojin da ke gudanar da shi, ba su yi kyakkyawan tunani ba.

Kadan daga cikin abin da kudirin ya kunsa, akwai kokarin saisaita tubabbu, gyara musu dabi’u, samar musu sana’o’in sake rayuwa a cikin al’umma, warware musu mummunar akida, yafewa da yin afuwa ga wadanda suka ajiye makaman su da sauran su.

Sanata Ago Akinyrlure daga Jihar Oyo, ya ce wannan kudiri ai mummunan tunani ne, wanda ma hankali ba zai amsa ba.

“Ta yaya za a kafa hukumar kula da Boko Haram, wai tubabbu, wadanda ake ikirarin cewa yawancin su ba ‘yan Najeriya ba ne? Wannan ai sagegeduwa ce kawai.”

Ya ce mugu dai mugu ne, kuma abokin gabar ka mai kashe ka ta nuna bambancin akida, ba mai taba shiryuwa ba ne.

Sai ya bada shawarar cewa har gara ma a yi amfani da kudin a gyara wuraren da Boko Haram suka lalata.

Shi ma Sanata Danjuma Laah daga Kaduna ta Kudu, ya ce bai goyi baya ba. Har ma ya ce an sha kama masu kunar bakin wake a cikin sansanin masu gudun hijira, wadanda a cikin sansanin suke rayuwa.

Tsoffin sanatoci Shehu Sani da Isa Misau, duk sun ki amincewa da kudirin, inda Sani ya ce ai gwamnati ta gama komai, kuma sanatocin da suka shude a zamanin sa, sun yi kokari sun kafa Hukumar Farfado da Yankin Arewa maso Gabas.

Share.

game da Author