Ali Baba A Gama Lafiya Fagge: Idan An zo Muku Da Labari Ya Kamata Kuyi Bincike, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad (SAW), da Iyalan sa da Sahabban sa baki daya.

Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun! Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun!! Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun!!!

Don Allah me yasa a yau muka zama zamu iya aikata komai domin mu farantawa wasu rai, ko don mu samu abun duniya?

Jiya na kalli wani bidiyo da yake yawo a kafafen yada labarai na zamani (wato social media), a inda wani mataimaki na musamman ko mai bayar da shawara na musamman ga gwamnan Jihar Kano, mai suna Ali Baba a gama lafiya Fagge yayi, kuma aka yada shi. A inda wannan mutum yake wasu irin maganganu da basu dace ba, yana kokarin jinginawa ga Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, duk da dai shima a cikin bidiyon yayi kokarin nuna cewa bai da tabbacin shin wadannan maganganu haka suke ko kuwa sharri da kazafi ne aka yiwa Mai Martaba Sarki!

A cikin maganganun sa ya kawo maganar ziyara da Mai Martaba Sarki ya kaiwa mai girma tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida (IBB). Har yake cewa wai Sarki ya kai wannan ziyara ce da nufin rokon mai girma IBB yasa baki a cikin shari’ar kotun koli don a kayar da gwamna Ganduje. To ina son don Allah, shi mai girma IBB ya fito ya fada wa duniya, shin haduwar su da Mai Martaba Sarki, don Allah sun yi maganar gwamna Ganduje ko maganar hukuncin da za’a yanke a kotun koli? Me ke damun wadannan mutane ne? Da basa tsoron Allah a cikin abun da zasu fada ko zasu rubuta, ko zasu yada, musamman ma idan akan Sarki ne? Shin su basu san da cewa Allah Subhanahu wa Ta’ala yayi umurni da yin adalci ba ne?

Sarki Sanusi in Minna

Sarki Sanusi in Minna

Sannan na biyu a cikin maganganun sa yace, wai Mai Martaba Sarki ya ziyarci wasu manyan mutane da dama a kasar nan, wai yana kokarin kamun kafa, da rokon su susa baki domin a kayar da gwamna Ganduje a hukuncin kotun koli. Kuma wai yake cewa Mai Martaba Sarki ya taka muhimmiyar rawa sosai, wurin ganin gwamna Ganduje bai samu nasara ba! Abun tambaya anan shine, don Allah, don Allah wadanne mutane ne Sarki ya kaiwa ziyara, har yayi maganar gwamna Ganduje da su? Ya kamata a gama lafiya, indai har kana neman gamawa da duniyar nan lafiya, to ka fito ka bayyana muna wadannan mutane. Ko kuma su mutanen su fito suyi bayani, kar su boye komai, su shaidawa duniya inda suka taba yin haka da Mai Martaba Sarki!

Wallahi, wallahi, wallahi ya kamata, kuma ya zama wajibi mu kasance masu tsoron Allah a cikin dukkanin abun da zamu fada ko zamu rubuta. Domin Allah zai tambaye mu akai!

Allah Ta’ala ya fada a cikin littafin sa mai tsarki cewa:

“يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنْ جَاءَكُمْ فَاسِقٌ بِنَبَإٍ فَتَبَيَّنُوا أَنْ تُصِيبُوا قَوْمًا بِجَهَالَةٍ فَتُصْبِحُوا عَلَىٰ مَا فَعَلْتُمْ نَادِمِينَ.”

“Ya ku waɗanda suka yi imani! Idan fasiƙi yazo maku da wani babban labari, to, ku nemi bayani, kuyi bincike, domin kada ku cutar da waɗansu mutane a cikin jahilci (rashin sani), saboda haka sai ku wayi gari a kan abin da kuka aikata kuna masu nadama.” [Suratul Hujurat, 6]

Abun mamaki, abin tausayi, kuma abun da yake matukar damun duk wani mai hankali, kuma yake daga masa hankali shine, irin yadda a kullum nike ganin mu Musulmai zuciyar mu ta ta’allaka matuka ga wadannan kafafen yada labaru na zamani (wato social media), kuma wasun mu ma suna yarda da duk irin abun da aka fada a cikin su ko aka rubuta, ko aka yada, musamman domin a cimma wani buri ko wata manufa ta tozarta wani ko bata masa suna, wadanda yawancin masu wannan aiki makaryata ne, kuma fasikai ne, marasa tsoron Allah da tunanin lahirar su. Sannan kuma duk wani abun da ya shafi addinin Musulunci ko yake da alaka da addinin Musulunci, to so suke yi su canza masa kamanni, su kakaba masa mummunan suna da wata irin mummunar sura. Sannan kuma duk wani abu da aka yi da sunan Musulunci to an rinka yayata shi kenan, amma har yanzu wasu Musulmai sun kasa gane hakan. Mun wayi gari duk abunda aka fada muna, ko aka bamu labari, yarda muke yi ba tare da yin bincike ba, wanda wannan ya sabawa koyarwar addinin mu na Musulunci.

A Musulunci, ko waye ne ya kawo maka labari, addinin Musulunci ya koyar damu, mu binciki gaskiyar sa tukuna, to ina ga kuma cewa wanda ya kawo labarin muna tuhumar sa da fasikanci? Wallahi ya kamata mu Musulmai mu zama wayayyu, kada ya kasance mun zama kidahumai, komai aka fada muna kawai mu yarda, mu bi.

Kirana ga dukkanin al’ummah shine, mu kiyaye bakunan mu daga fadar komai da muka ji, ko muke karantawa, har sai mun samu yakini cewa gaskiya ne. Domin yawancin bayin Allah da ake shiga kafafen yada labarai ana bata masu suna, wallahi da zaka yi bincike, da za ka bibiyi yadda suke tafiyar da al’amurran su, sai ka sami akasin abun da ake yadawa na karya akan su.

Sannan me yasa duk abun da ya shafi masarautun mu masu daraja, na Musulunci, sai a rinka kokarin yada sharri, ana neman bata masu suna? Lallai ya zama wajibi mu natsu, mu shiga taitayin mu, mu san me muke yi. Duk irin wadannan labarai na kanzon kurege, da bamu da hakikani da tabbacin faruwar su ya kamata mu daina yarda da su, har sai mun sami hujjoji da dalilai, domin haka ne kadai zai tseratar da mu a gobe kiyama, gaban Allah. Domin mu sani, wallahi duk wani abun da zamu fada, ko mu rubuta, ko mu shiga kafafen yada labarai mu yada bidiyon sa ko audiyon sa, to yana nan ajiye yana jiran mu, za mu zo muyi bayanin sa a gaban Allah. Kar mu dauka cewa duk abunda muka rubuta ko muka fada mun ci bilis, shike nan ya wuce, wallahi sam ba haka ba ne!

Kai jama’ah, haka jiya fa naga wasu miyagu, makirai suna yada wani labarin karya, wanda ya cika ko’ina, cewa wai Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II yayi murabus. Wasu ma cewa suka yi har Sarkin ya gabatar da takardar murabus ga gwamnatin Jihar Kano. Kuma wai Mai Martaba Sarki yana kokarin sulalewa ya bar kasar. Alhali a lokacin da suke yada wannan karyar, kowa yasan da cewa Sarki yana Abuja wurin taron da ya shafi tattaunawa tsakanin Musulmai da abokan zaman su Kiristoci, don samar da zaman lafiya, sanadiyyar abubuwan da suke faruwa a kasar nan. Amma da yake su wadannan mutane har kulkun ba alkhairi suke nema ba, sun yada cewa wai Sarki yayi murabus, kuma yana neman hanyar barin kasar!

Hatta ziyarar da Mai Martaba Sarki ya kai wa mai girma tsohon shugaban kasa IBB a Mina, mutanen banza sun juya ta cewa wai Sarki ya kai wannan ziyara ne, domin ya roki IBB wai yasa baki domin a kayar da gwamna Ganduje a shari’ar da aka yanke hukunci a kotun koli. Alhali duk wani mai hankali, adali, yana sane cewa Islamic Education Trust ne, wato IET, suka gayyaci Mai Martaba Sarki taron su na cikar shekaru hamsin da kafuwa, shine Sarki ya ziyarci IBB domin a gaisa. Kasancewar duk wani mai hankali yasan cewa bai kamata ace IBB yana gari, har Sarki ya shiga Mina ya fita, ba tare da sun gaisa ba. Sannan idan ba gaskiya bane muke fada, ai IET din suna nan, sannan shi kan sa IBB din yana nan raye, idan ba haka bane don Allah, don Allah su fito su karyata, suce ba haka ba ne!

Duk abun da wadannan mutane suke tunani game da Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, sam ba haka yake ba. Domin shi mutum ne mai dogaro ga Allah, mai tawali’u, mai kiyayewa game da al’amurra. Mutum ne da baya rike mutane a zuciyar sa. Komai nasa yana bar wa Allah ne. Mai yafiya ne, shi ba mai ramuwa ba ne, ko mai daukar fansar abun da ake yi masa. Domin da ace shi mai ramuwa ne akan irin bita da kulli da ake yi masa, da an ga hakan. Domin kowa yasan cewa an nemi a tozarta shi, aci mutuncin sa, a sauke shi daga sarautar Kano; an kirkiro wasu masarautu, domin dai duk a musguna masa, amma da yake shi Allah ne a gaban sa, kawai duk ya bar mutane da Allah. Domin wadannan abubuwa da ake yi masa ai yana da yanci da dama da iko na kare kansa, amma sai bai yi hakan ba, ya bar su da Allah, domin shi yana da cikakken yakinin cewa Allah ya isar masa a komai!

Ina rokon Allah ya kyauta, kuma ya kawo muna mafita ta alkhairi, kuma ya ganar da wadannan mutane hanyar gaskiya, kuma ya basu ikon bin ta, amin.

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author