Sakamakon binciken da kungiyar kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi ya nuna cewa kashi 15 zuwa 58 na mutane a Najeriya na yawan kamuwa da cututtukan dake kama hakora.
Binciken ya kuma kara nuna cewa kashi 30 bisa 100 daga cikin su kan dade suna fama da wadannan cututtuka ba tare da sun je asibiti ba.
Hakan na da nasaba ne da rashin wanke hakora yadda ya kamata da mutane ke yi.
Bayan haka sakamakon binciken da ‘National Smile Mouth’ ta gudanar ya nuna cewa mutane Biyu cikin mutane Uku a Najeriya basu da masaniya game da yadda ya kamata wanke baki da hakora.
A dalilin haka wani likita a shafinsa na tiwita yayi kira ga mutane da su daina kuskure baki da ruwa kaf bayan an goge hakora da man goge hakorar cewa dan barin kumfar na kara inganta tsaftar baki da karfin hakorar.
Fadin haka da wannan likita ya yi ya sa (Shafin Dubawa) dake yanar gizo ta yi hira da wani likita domin samun karin bayani game da haka.
A hirar da suka yi da wani likitan hakora dake Jami’ar Maiduguri jihar Barno Lawal Balami ya tabbatar da haka inda ya kara da cewa rashin sani na daga ciki matsalolin dake haddasa cututtukan hakora da mafi yawan mutane a Najeriya ke fama da su.
Ya kara da cewa ya kamata mutum ya wanke hakorar sa sau biyu a rana sannan a duk wanki a dauki akalla mintuna biyu ana goge hakora.
Sannan kuma barin kumfar man goge baki a cikin baki na inganta aikin sinadarin ‘Fluoride’ da ka yi man da shi.
Ya ce sinadarin fluoride sinadari ne dake karfafa karfin hakorar mutum, hana warin baki sannan da kare hakora daga kamuwa da cututtuka.
Lawal ya ce idan za a iya a daina kuskure baki bayan a kammala gogewa, mai makon haka a yi amfani da ruwan ‘Mouth wash’ a wanke hakora da shi.