A raba aure na da miji na ko in kashe shi – Inji Matan Aure a Abuja

0

A ranar Litini ne wata matar aure mai suna Ruth Peter ta nemi kotun Nyanya, Abuja da ta raba auren ta da mijinta Peter ko ta kashe shi.

A bayanin da ta yi Ruth ta ce mijinta Peter na da saurin fushi domin a kusan kullum sai ya lakada mata dukan tsiya.

“ Wata rana da muka yi fada da mijina, sai ya shake ni kamar zai kashe ni, daga nan sai ni kuma na falla da gudu zuwa dakin dafa abinci na dauko wuka na caka masa a hannu.

“ A yanzu haka bani da hakurin iya jure azabtar dani da yake yi, idan ba a raba auren ba zan iya kashe shi.

Mijin nata Peter ya karyata duk abin da Ruth ta fadi a gaban Alkali, sai dai ya ce yanzu ya daina abubuwan da matarsa take zargin sa dashi.

Peter ya ce yayi nadama sannan ya roki kotu da kada ta raba auren sa da Ruth cewa har yanzu yana matukar sonta.

A karshe ya Alkalin kotun ya umarci su duka su koma gida su zauna a teburin sulhu don sasantawa da kan su.

Za a ci gaba da shari’ar ne ranar 30 ga watan Janairu.

Yadda Rabi ta kasha Mijinta Shamsuddeen a jihar Katsina

A ranar litinin ne wata matan aure mai suna Rabi Shamsuddeen dake da shekaru 19 ta kashe mijinta da sharbebiyar wuka a karamar hukumar Malumfashi, Jihar Katsina.

Rabi da mijinta Shamsuddeen Salisu na zaune ne a kauyen Danjanku-Tasha dake karamar hukumar Malumfashi, a jihar Katsina.

Makwauta da suka bayyana wa ‘yan sanda abinda ya faru sun shaida cewa sun rika jin Ihun Sahamsuddeen, wato mijin Rabi yana kira da azo a taimake shi, a kawo masa dauki.

Ko da makwautan suka dunguma cikin gaggawa zuwa gidan Shamsuddeen sai suka iske an datse kyauren gidan da kwado ta ciki.

Daga nan ne fa wasu suka yi kukan kura suka haura ta katanga, fadawar su ke da wuya sai suka iske mijin Rabi wato Shamsudden kwance malemale cikin jini, yana mirgina jiki, ita kuma Rabi tsaye a kan sa da sharbebiyar wuka duk jini ta na kallon su.

Wadannan makwauta sai suka yi gaggawar daukar Shamsuddeen zuwa asibiti domin ceto ran sa, sai dai kash, isar su ke da wuya sai likitoci suka ce ai ya cika.

Kakakin ‘Yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah ya yi karin bayani a kai in da ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya tuni ‘yan sanda sun fara bincike akai, cewa da zarar ta kammala haka za a gurfanar da rabi a gaban kuliya manta sabo.

Kotu ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin rataya

Kotu a Abuja ta yanke wa Maryam Sanda wanda ta kashe mijinta da wuka hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Idan ba a manta ba a shekarar 2017 ne rundunar ‘yan sanda da shigar da kara Kotu kan kashe mijinta da wuka da Maryam tayi.

Mijin Maryam, Biyaminu Halliru dan tsohon shugaban jam’iyyar PDP ne Bello Halliru.

Maryam ta musanta cewa ita ce ta kashe, ta bayyana cewa sun kaure da fada ne bayan ta ga wasu hutunan mata sirara a wayar sa. Daga nan ta nemi a yayi mata bayani akai sai suka kaure da fada.

Ta ce a daidai haka ne tulun shishar da ajiye a dakin ya do ya fashe, shi kuma marigayi Bilyaminu ya yanke jiki ya fadi a kai, ya mutu.

Sai dai kuma a binciken da kotu tayi da bayanan da ‘yan sanda suka mika a gaban kotun, ya tabbata cewa wuka ce Maryam ta daba wa Bilyaminu.

Alkalin kotun Mai shari’a Yusuf Halilu, ya kara da cewa wannan bayani da mai kare mai laifi yayi shirya shi aka yi don a yi wa kotu rufa-rufa, amma abin da ya tabbata shine lallai Maryam ce ta daba wa mijinta wuka.

Bayan mai shari’a ya yanke hukunci, sai Maryam ta zabura a guje ta nemi ficewa da ga kotu, sannan ‘yan uwanta suka fara kuwwa suna tsalle da koke-koke.

Daga baya dai da komai ya lafa sai alkali ya ci gaba da karatun hukuncin sa.

Share.

game da Author