IRAN: Mutune 40 sun mutu wurin tirmitsitsin jana’izar Qassem Soleimani

0

Akalla mutane 40 suka mutu a wani tirmitsitsi da ya faru wurin jerin gwanon jana’izar gawar Janar Qassem Soleimani da sojojin Amurka suka kashe.

Tirmitsitsin ya faru a birnin Kerman na Iran a yau Talata.

An kuma ruwaito cewa sama da mutane 200 suka ji rauni, kamar yadda gidan talbijin na Al’jazira ya ruwaito Kamfanin Dillancin Labarai na Fars ya bayyana a yau Talata.

“ Ya zuwa yanzu dai mutane 40 suka rasu sannan wasu 213 suka ji raunuka.” Haka jami’in ya ruwaito, kuma ya ce “tirmitsitsin yawan jama’a ne ya yi sanadiyyar mutuwar ta su.”

Jami’ai sun ce an dage jana’izar har zuwa wata ranar da ba a bayyana ba zuwa yanzu tukunna.

An dage jana’izar ganin yadda dimbin dubun dubatar jama’a suka cika manyan titinan biranen Ahvez na kudu maso yammacin Iran da Mashhad da ke arewa maso yamma da Teheran da kuma birnin Qum mai dimbin tarihi.

Kisan Soleimani ya haifar da fargabar barkewar kazamin yaki tsakanin Amurka da Iran, wanda ake hasashen cewa ka iya zama yakin duniya na uku.

Tuni dai a Najeriya Majalisar Kolin Addinin Musulunci, NSCIA ta roki mafusatan matasa da su kai zuciya nesa kada su gudanar da zanga-zangar da aka ce sun a shirin gudanarwa ta lumana a Najeriya.

A Iran kuwa, wanda ya shirya zanga-zanga da jerin-gwanon jana’izar Qassem Soleiman ya yi kira ga al’ummar kasa kowa ya bayar da gudummawar dala 1 tal, domin a tara dala milyan 80, wadda za a biya a matsayin lada ga duk wanda ya kashe Shugaban Amurka Donald Trump.

Share.

game da Author