Tsohon Sanatan da ya wakilci Shiyyar Abia ta Arewa a Majalisar Dattawa da ta gabata, Sanata Mao Ohuabunwa, ya bayyana cewa da-na-sani da bakin cikin da ya ke yi dangane da kulle tsohon gwamnan jihar Abia Sanata Kalu da aka yi, shi ne yadda aka yi watsi da ayyukan inganta rayuwar al’umma da aka fara yi lokacin da ya na majalisa a mazabar sa.
Ohuabunwa wanda shi ne kan kujera 2015 zuwa 2019, ya tsaya takarar Sanata tare da Uzor Kalu, a karkashin APC, amma Kalu ya kayar da shi a zaben fidda-gwanin jam’iyyar.
An daure Kalu shekaru 12, bayan samun sa da kotu ta yi da laifin harkallar naira bilyan 7.56.
Da ya ke tattaunawa da manema labarai a Umuahia, jiya Litinin, domin murna da shigowar sabuwar shekara, Ohuabunwa ya ce ya na fargabar da wahala a ci gaba da gudanar da ayyukan raya al’umma da Kalu ya fara a mazabar sa, domin a yanzu mazabar ba ta da wajilci a Majalisar Dattawa.
“Ina bakin ciki da da-na-sanin rashin wakilcin da Abia ta Arewa ba ta da shi a Majalisar Dattawa. Ina cikin damuwa sosai, domin wannan mazaba ta mu ba ta da wakilli yanzu a Majalisar Dattawa a Abuja.
“Ina da ayyukan raya kasa da na fara, kuma ni da fata na idan na samu komawa majalisa a zaben 2019, to zan ci gaba da wadannan ayyuka.”
Ya ce musamman ya fi damuwa da tsaikon ayyukan inganta lafiya, wanda za a gina cibiyoyin lafiya a yankin, wadanda aka giggina a yankuna da dama, ake jiran budewa a ke jiran a zuba musu kayayyaki.
Bayan ya lissafa ayyukan da ya ce ke kan hanya wadanda aka yi watsi da su, ko kuma ya ke fargabar ba za a karasa ba, sai ya yi kira ga al’ummar yankin su tashi tsaye su nemi sanin halin da kujerar mazabar ke ciki, domin a rika damawa da su a halin yanzu.