Wani mamban kwamitin inganta kiwon lafiya na masarautar Kano (KECCHD), Dayyabu Muhammad ya bayyana cewa kashi 48 bisa 100 na yara a jihar Kano na fama da matsanancin yunwa.
Muhammad ya fadi haka ne a taron da KECCHD da UNICEF suka shirya domin samar da mafita game da matsanancin yunwa da yara ke fama da shi a jihar.
Ya ce an shirya wannan taro ne domin wayar da kan sarakuna da uwaye kan irin rawar da za su iya takawa wajen ganin an kawar da yunwa a jikin yara.
Muhammad ya kuma kara da cewa sakamakon binciken da KECCHD ta gudanar ya nuna cewa kashi 41.3 na yara kanana musamman ‘yan watanni shida zuwa shekara biyu a karamar hukumar Sumaila na fama da yunwa.
Sannan a karamar hukumar Bichi an gano cewa yara kanana kashi 38.1 na fama da yunwa a jihar.
Idan ba a manta ba a watan Satumbar 2019 ne gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ta kashe akalla Naira biliyan 1.8 don ciyar da yara kanana dake fama da matsanancin yunwa a jihohi 18 dake kasar.
Shugaban sashen yaki da kawar da yunwa na ma’aikatar kiwon lafiya Chris Isokpunwu yace gwamnati ta kashe wadannan kudade ne tsakanin shekaru 2017 zuwa 2018.
Isokpunwu ya bayyana cewa sakamakon binciken da ma’aikatar kiwon lafiya ta gudanar a 2017 ya nuna cewa jihohi 18 a kasar nan na fama da matsanancin yunwa.
Ya ce a dalilin haka gwamnati ta tsaro matakai tare da hada hannu da Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya (UNICEF) domin ganin ta kawo karshen wannan matsala a Najeriya.
Discussion about this post