AMOTEKUN: Ba za mu rushe rundunar tsaron mu ba, suna nan daram-dam – Gwamnan Oyo

0

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa Jihohin Kudu maso Yamma ba za su ruguza rundunar Amotekun da suka kafa kwanan nan ba.

Makinde ya ce kafa rundunar ya biyo bayan babbar matsalar karancin jami’an ‘yan sanda wadanda babu wadatar su a cikin lunguna da kauyukan kasar nan.

Gwamnonin Jihohin Yarbawa shida da su ka hada da Seyi Makinde (Oyo), Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Gboyega Oyetola (Osun) Kayode Fayemi (Ekiti) Rotimi Akeredolu (Ondo) da Dapo Abiodun (Ogun) ne suka hadu suka kafa rundunar makonni biyu da suka gabata.

Tun bayan da kafa rundunar ce ake ta maganganu dangane da dacewa ko rashin dacewar kafa ta.

Yayin da gwamnonin johohin ke cewa sun kafa rundunar ce domin dakile manyan laifuka da suka hada da fashi da garkuwa da mutane a yankunan su, ta hanyar taimaka wa jami’an ‘yan sanda.

Sai dai kuma gwamnatin tarayya ta bayyana cewa kungiyar haramtacciya ce.

Shi kuwa Gwamna Makinde, ya ce ai alkalami ya rigaya ya bushe, domin ba za su taba ruguza Amotekun ba.

Yayin da ya ke wa Kungiyar Matasan Yarabawa Zalla ta Duniya jawabi a yau jiya Talata, Makinde ya ce wannan rungunar tsaro ba wani sabon abu ko wani mugun nufi za ta rika yi ba.

Ya ce za ta rika gudanar da tsaro da sintiri ne musamman a wuraren da babu ‘yan sanda kwata-kwata, sai kuma taimaka wa ’yan sanda da bayanai ko rahotanin wasu matsalolin tsaro da ke da bukatar ’yan sanda su dakile cikin gaggawa.

Makinde wanda ya yi jawabi ta bakin Kakakin Yada Labaran sa, Bisi Ilaka, ya jaddada cewa zanga-zangar da matasan suka yi ta kara sa musu kwarin guiwar daukar rungunar Amotekun da muhimmancin gaske.

Daga nan ya ce ba za su taba maida hannun agogo baya, su rushe Amotekun bayan sun rigaya sun kafa rundunar, kuma sun shirya tafiyar da ita domin tabbatar da tsaro a yankunan su.

Ya kara da cewa kowa a kasar nan ya san ana fama da karancin ’yan sanda. Kuma kowa ya san babu ’yan sanda a wurare da yawa a kasar nan, musamman a cikin yankunan karkara.

Don haka ya zama wajibi a tashi tsaye a kafa rundunar tsaron da za ta rika aikin taimaka wa ’yan sanda da kuma samar da tsaro a yankunan da ba a ma taba tura ’yan sand aba kwata-kwata.

Share.

game da Author