Sakamakon wani bincike da aka yi ya nuna cewa mai shan taba ba zai kamu da matsalolin da akan yi fama da su ba bayan anyi wa mara lafiya fida idan ya daina shan taba na tsawon wata daya kafin a yi masa aikin.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO), jami’ar Newcastle dake kasar Australia da kungiyar likitoci masu yin fida ta duniya (WFSA) ne suka gudanar da wannan bincike.
Wani likita dake fannin wayar da kan mutane sanin illar dake tattare da shan taba na kungiyar WHO mai suna Vinayak Prasad ya bayyana cewa taba na dauke da sinadarin ‘Nicotine da Carbonmonoxide’ wanda ke kawo cututtukan dake kama zuciya da lalata huhu.
Sannan taba na rage karfin garkuwar jikin mutum da ke sa ciwo ko rauni kin warkewa da wuri.
Sannan binciken ya nuna cewa idan mai shan taba ya kauracewa wa shan taba na tsawon mako daya zuwa makonni hudu ingancin kiwon lafiyar sa na karuwa zuwa kashi 19 bisa 100.
“ Hakan na nuna cewa a duk lokacin da aka yi wa mai shan taba aikin fida to lallai zai yi fama da matsalar rashin warkewar wurin da aka yi masa fida.
“ Mai shan taba zai iya guje wa wadannan matsaloli idan ya kaurace wa shan ta na tsawon wata daya kafin a yi masa aikin fida.
Wani jami’in WHO Shams Syed ya ce sakamakon wannan bincike zai taimaka wa masu shan taba wajen dakata wa idan ya kai ga sai an yi musu fida kan wani aiki a jikin su.
Sannan hakan na iya taimaka wa mutane dake shan taba rabuwa da taba kwata-kwata.