Akalla mutane uku sun rasu a jihar Kano a dalilin kamuwa da Zazzabin Lassa da suka yi.
Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Aminu Tsanyawa ya bayyana haka da yake hira da manema labarai a garin Kano ranar Laraba.
Tsanyawa ya bayyana cewa wata mata mai ciki da likitoci biyu da suka duba ta a asibiti suka rasu.
Bayan haka ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar ta killace wasu mutane har 292 da suka yi hulda da wannan mai ciki kafin ta rasu.
Tsanyawa ya ce dukkan su na killace a wasu wurare domin a duba su gudun kada cutar ya yadu. Bayan nan yayi kira ga mutane da su mai da hankali wajen kula da muhallin su da tsaftace shi. Sannan kuma su rika gujewa cin nama ba tare da sun tabbatar da tsaftar shi ba kuma a rika dafa nama sosai.
Jihar Ondo
Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya bayyana cewa rashin tsaftace muhalli na daga cikin matsalolin da ya sa zazzabin lassa ke ci gaba da yaduwa a jihar.
Bayannan gwamnan ya kara da cewa rashin adana abinci, wankan gawa a gida, rashin zubar da shara, kona daji da sauran su duk na daga cikin matsalolin dake sa cutar da ci gaba da yaduwa.
Ya kara da cewa a cikin makonnin da suka wuce mutane 16 sun rasu a dalilin kamuwa da cutar sannan mutane sama da 80 na nan a kwance a asibitocin kula da wadanda ke dauke da cutar.
Ya ce kananan hukumomin da suka hada da Akoko ta Kudu maso Yamma, Owo, Akure ta Kudu da Ondo ne kananan hukumonin da cutar ke yawo.
Akeredolu ya ce gwamnati za ta maida hankali wajen ganin ta dakile yaduwar wannan cuta a jihar.