Wani fasto mai suna Denis Bagauri wanda aka fi sani da kira da ‘Fastor Nyako’ ya gamu da ajalinsa a hannun wasu mahara da suka afka har cikin gidan sa da dare suka kashe shi.
Fastor Nyako na zaune ne a unguwar Nasarawo Jereng dake karamar hukumar Mayo Belewa, jihar Adamawa.
Wani mazaunin garin da baya so a fadi sunan sa ya bayyana cewa ‘Fastor Nyako’ dan siyasa ne da ya yi aiki tare da tsohon gwamna Murtala Nyako da tsohon gwamnan jihar Jibrilla Bindow a matsayain mai taimaka musu a harkokin addini.
Mafarin samun sunan sa kenan wato ‘Fastor Nyako’.
Shugaban kungiyar makiyaya ‘Miyetti Allah’ dake jihar kuma abokin marigayin Muhammad Buba ya ce abokin sa Bagauri mutum ne da ya san daraja da mutuncin mutane inda hakan ya sa yake hulda da kowa da kowa sannan kuma kowa na yaba masa.
Ya kara da cewa lallai sun yi matukar rashin Fasto Nyako.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Suleiman Nguroje ya tabbatar da aukuwar wannan al’amari sannan ya kara da cewa rundunar za ta fitar da cikakken bayani kan ainihin abinda ya faru sannan kuma yayi kira ga mutane da su zauna lafiya sannan su rika ankarewa a duk lokacin da suka ga ba daidai ba.