SHARI’AR KANO: Ganduje ya nemi hadin kai, PDP ta ce ‘wata shari’a sai a lahira’

0

Gwamnan Jihar Kano AbdullaHI Ganduje ya roki ’yan adawa su ajiye adawa, su zo a taru a gina jihar Kano baki daya.

Ganduje ya yi wannan jawabi ne bayan da Kotun Koli ta jaddada nasarar sa a kan wanda ya kais hi kara, Abba Yusuf na PDP.

Kakakin Yada Labarai na Ganduje, Abba Anwar, ya bayyana cewa Ganduje ya gode wa Allah dangane da jaddada nasarar sa da Kotun Koli ta yi a yau Litinin.

Daga nan kuma ya gode wa al’ummar jihar Kano saboda zaman lafiyar da suka zaba, ba tare da tayar da tarzoma ba.

Daga nan kuma Ganduje ya gode wa alkalai bakwai din da suka jaddada nasarar sa, ya ce hakan ya kara wa dimokradiyya karsashi.

“Ina nan a kan baka na cewa masu adawa su zo mu hadu mu ciyar da jihar Kano gaba. Muna da ayyukan ci gaban kasa da a yanzu haka mu ke kan aiwatarwa da ma wadanda ba mu far aba. Akwai bukatar kowa ya zo ya sa hannu wajen kara samar da tsaro da harkokin ilmi a jihar Kano.”
Inji Ganduje.

A na ta raddin, jam’iyyar PDP ta bayyana hukuncin da alkalan Kotun Koli su bakwai a karkashin Cif Jojin Najeriya, Tanko Muhammad suka yi cewa fashi da makami ne suka yi wa jam’iyyar PDP a jihar Kano.

Sanusi Dawakin Tofa ya bayyana cewa, “A yanzu dai mun ga irin tsiyar da duk za su iya tabkawa, kuma sun tabka din.

Shari’a kuma sai a lahira a gaban Allah. Wannan ranar kuwa za a yi musu hukuncin ba za su iya tsallakewa ba.”

Share.

game da Author