Duk da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa jam’iyyar adawa garin cewa, “Su masu adawa sai zaben da suka yi nasara ne kadai zabe na kwarai”, sai ga shi bayan da Kotun Koli ta bayyana sakamakon hukuncin jihohi hudy a jiya Litinin, Buhari ya taya gwamnonin APC biyu murna, amma bai taya biyu na PDP da suka yi nasara ba.
Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Jam’iyyar APC da Gwamna Abdullahi Ganduje da Simon Lalong murnar nasara a Kotun Koli.
Cikin sanarwar da Garba Shehu, Kakakin Yada Labaran gwamnatin sa ya fitar jiya, Buhari ya jinjina wa Shugabannin APC saboda irin biyayyar da suke bayarwa ga tafiyar jam’iyar APC.
Ya ce irin biyayyar da shugabannin ke bayarwa da kuma jajircewa sun haifar da nasarorin da APC ke samu musamman a jihohin da ke da muhimmanci a siyasa, musamman Kano da Filto.
“ Na yi farin ciki da irin yadda duk da an keto daji mai nisa, a karshe dai gwamnonin mu sun yi nasara. Dama APC din ce ta lashe zabukan, to kuma hakan ya kara tabbata a Kotun Koli.
“ Da APC ba ta yi nasara a muhimman jihohi kamar Kano da Filato ba, to da an yi mana dukan da ba mu iya mikewa.”
Daga sai ya roki shugabanni da masu zabe su kara taimakawa a karfafa fannin shari’a.
“Su masu adawa sun dauki dabi’ar sai zaben da suka yi nasara ne kadai zabe na kwarai. Amma kuma ba haka ya kamata a kalli al’amarin nan ba.
“ Ita dimokradiyya ba wai ta tsaya ne kadai a kan wadanda suka yi nasara ko wadanda suka fadi ba. Ita abu ce da ake ci gaba ko da yaushe.
Idan masu adawa na yin tir da kowane irin hukuncin kotu, to kamar su na yin tir da dimokradiyyar ce baki daya.”
Sai dai kuma duk da wannan nasihar da Buhari ya yi wa masu adawa, shi ma sai dai gwamnonin APC kadai ya taya murna, amma bai taya gwamna Tambuwal da Bala Mohammed na Sokoto da Bauchi ba, saboda su ’yan PDP ne.