Wata sabuwar bincike da wani likita mai suna JoAnne Flynn dake jami’ar Pittsburgh Pennsylvania ya gano cewa yi wa mai fama da tarin fuka allurar BCG a jijiya na sa maganin yin oaiki matuka a jikin mutum.
Allurar BCG allura ce da ake yi don rigakafin cutar tarin fuka.
Sakamakon bincken Flynn ya nuna cewa maganin BCG ya fi yi wa mutum aiki a jiki da samar masa da kariya fiye da idan an yi wa mutum allurar a jikin sa kamar yadda aka saba.
Idan ba a manta ba binciken da aka yi a shekarar 2019 game da wannan cuta ya nuna cewa mutane miliyan 10 ne suka kamu da tarin fuka a duniya a shekaran 2018.
Daga cikin su akwai maza miliyan 3.2, mata da yara kanana miliyan 1.1 sannan masu dauke da cutar kanjamau sun kai kashi 9 bisa 100 na mutanen duniya.
Bayan haka binciken ya nuna cewa an samu ragowar yawan mace-macen mutanen dake dauke da wannan cuta a shekaran 2018. Domin a 2018 mutane miliyan 1.5 ne suka rasu sannan a 2017 mutane miliyan 1.6.
Hakan na da nasaba ne da yadda asusun hana yaduwar cutar da sauran kungiyoyin bada tallafi suka zage damtse wajen kula da mutane miliyan bakwai dake dauke da cutar.