A ranar litinin ne wata matan aure mai suna Rabi Shamsuddeen dake da shekaru 19 ta kashe mijinta da sharbebiyar wuka a karamar hukumar Malumfashi, Jihar Katsina.
Rabi da mijinta Shamsuddeen Salisu na zaune ne a kauyen Danjanku-Tasha dake karamar hukumar Malumfashi, a jihar Katsina.
Makwauta da suka bayyana wa ‘yan sanda abinda ya faru sun shaida cewa sun rika jin Ihun Sahamsuddeen, wato mijin Rabi yana kira da azo a taimake shi, a kawo masa dauki.
Ko da makwautan suka dunguma cikin gaggawa zuwa gidan Shamsuddeen sai suka iske an datse kyauren gidan da kwado ta ciki.
Daga nan ne fa wasu suka yi kukan kura suka haura ta katanga, fadawar su ke da wuya sai suka iske mijin Rabi wato Shamsudden kwance malemale cikin jini, yana mirgina jiki, ita kuma Rabi tsaye a kan sa da sharbebiyar wuka duk jini ta na kallon su.
Wadannan makwauta sai suka yi gaggawar daukar Shamsuddeen zuwa asibiti domin ceto ran sa, sai dai kash, isar su ke da wuya sai likitoci suka ce ai ya cika.
Kakakin ‘Yan sandan jihar Katsina, Gambo Isah ya yi karin bayani a kai in da ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya tuni ‘yan sanda sun fara bincike akai, cewa da zarar ta kammala haka za a gurfanar da rabi a gaban kuliya manta sabo.
Idan ba a manta ba, A ranar titini ne kotu a Abuja ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kotu ta bayyana cewa ya tabbata Maryam ta kashe mijinta, Bello Halliru da gangar.