‘Yan Arewa, Fushin Allah Ne Muka Tsokano, Ya Zama Wajibi Mu Tuba, Mu Koma Ga Allah, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Dukkan kyakkyawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad (SAW), da Iyalan sa da Sahabban sa baki daya.

Ya ku ‘yan uwana ‘yan yankin arewacin Najeriya, lallai ya zama wajibi mu sani, rikicewar da yankin mu na arewa yayi yana da alaka da tsokano fushin Allah da muka yi ta hanyar yin fito-na-fito da Allah, da taka dokokin sa, da afkawa cikin zunuban da ya haramta; zunuban da a tarihin Musulunci, muna sane da cewa, Allah ya halakar da al’ummomi da dama saboda su. Sanadiyyar haka sai Allah yayi fushi da mu, ya juya muna baya, ba domin komai ba sai don irin barna da wadannan zunuban da muke aikata wa.

Idan za mu iya tunawa, ai a da, can baya, kowa yasan yankin mu na arewa yafi ko’ina zaman lafiya, jin dadi da walwala. Duk wata damuwa da matsala sai dai mu ji labarin sa a wasu wuraren, to amma a halin yanzu dubi irin halin da muka samu kawunan mu a ciki don Allah!

Hukuma da dukkan jami’an tsaron ta kadai, wallahi ba zasu iya kawo muna karshen wadannan matsaloli ba. Har sai idan mun yarda cewa zamu taimaka masu da addu’o’i, da kuma canza halayen mu da dabi’un mu munana, ta hanyar tuba, neman gafarar Allah da komawa gare shi!

Allah Subhanahu wa Ta’ala ya tabbatar muna a wurare masu yawa a cikin littafin sa mai tsarki cewa, lallai duk abunda muka gani na fitintinu da musibu da bala’o’i iri-iri, to mune muka jawo wa kawunan mu shi, saboda butulce wa ni’imomin Allah da muke yi. Kuma Allah ya tabbatar muna cewa idan muka tuba, muka gyara, muka koma masa, muka yi nadamar abun da muke yi marar kyawo, to lallai zai canza muna wadannan damuwowi zuwa alkhairi!

‘Yan uwa na masu girma, don Allah zan tambaye mu, shin daga cikin zunubai da laifukan da Allah ya hane mu, wane laifi ne a yau ba’a aikata wa a yankin mu na arewa? Misali: Shirka, rashin biyayya ga iyaye, kisan kai da zubar da jinin bayin Allah, sihiri, wasa da sallah, kin biyan zakkah, kin yin azumin Ramadan da gangan ba tare da wani uzuri ba, kin yin aikin hajji alhali mutum yana da halin zuwa, yanke zumunta, zina, luwadi, cin riba, cin dukiyar maraya ko marayu, yiwa Allah da Manzon sa (SAW) karya, gudu daga filin daga, girman kai da alfahari, shaidar zur, shan giya, shan kwayoyi, caca, yiwa bayin Allah sharri da kazafi, satar dukiyar ganima da dukiyar gwamnati, sata, fashi da makami, rantsuwar karya, zalunci, tara dukiyar haram ta ko wane hali, cin haram, kisan kai, mutum ya kwanta da ‘yar sa ta cikin sa, yawan yin karya, zalunci a cikin shari’a, karbar cin hanci da rashawa, namiji yayi shigar mata, mace tayi shigar maza, shigar tsiraici ga mata, auren halatta mace ga tsohon mijinta, neman matan mutane, rashin yin tsarki da kyau, riya, neman ilimin addini don tara abun duniya, boye ilimi, cin amana, gori, kin yarda da kaddarar Allah, sauraron firar mutane ba tare da sanin su ba, yada jita-jita da annamimanci, karya alkawari, yin imani da aikin bokaye, aikata bokanci da tsibbu, mace ta wulakanta mijinta, namiji ya wulakanta matarsa, rashin hadin kai da rarrabuwa kungiya-kungiya, gina gumaka, yin kururuwa lokacin mutuwa, wulakanta mutane, mutum yaci amanar yaran aikin sa ko bayin sa, cutar da makwabci, zagi da cutar da musulmi, yiwa mutane girman kai da alfahari, jan tufafi a kasa da taka wando, maza suna sa tufafin alharini da sanya zinari, yanka domin tsafi, mutum ya danganta kan sa ga iyayen da ba nasa ba, yin rowar ruwa, tauye mudu da ma’auni, amincewa da azabar Allah, cutar da bayin Allah salihai da waliyan Allah, kin yin sallah a cikin jam’i, kin yin sallah cikin lokaci, kin yin sallar juma’ah, yaudara, ha’inci, leken asirin musulmi, zagin sahabban Annabi (SAW), shaye-shaye, wulakanta addinin Allah, wulakanta ‘ya ‘yan mu muki yi masu tarbiyyah, ha’incin masu mulki da ‘yan siyasa, manya ba sa tausayin na kasa da su, su kuma na kasa ba sa girmama manya, raina manya da cin mutuncin masu mutunci!

A cikin wadannan laifuka wane daga cikin su ne bamu aikatawa a arewacin Najeriya don Allah? Don haka ya rage namu, idan munji tsoron Allah mun tuba, mun gyara, sai Allah ya tausaya muna, ya canza muna wannan hali mara kyau da muka samu kawunan mu a ciki. Idan kuwa mun ki, to fa shi Allah babu ruwansa da mu wallahi!

Ya zama dole mu fahimci cewa sabon Allah ko aikata zunubi yana da illoli masu yawa ga ma’abotan sa, illolin da suna iya rusa al’ummah baki daya. Daga cikin illolin kuwa akwai:

1. Zuciya za ta kasance mai gadar da mugunta da zalunci da kaskanci da cutarwa; kuma ta kan kange bawa daga Ubangijin sa a duniya kuma tana gadar da makamancinta a lahira, kuma tana hana biyayya ga Manzon Allah (SAW).

2. Sabon Allah, aikata zunubi da kin bin umurnin Allah yana hana arziki, yana jawo wa al’ummah talauci, kaskanci da wulakanci, kuma yana gusar da ni’ima kuma yana gusar da albarkar dukiya.

3. Sabon Allah ko aikata zunubi yana tafiyar da albarkar rayuwa.

4. Sabon Allah ko aikata zunubi yana hana karbuwar ayyukan bawa a wurin Allah mahaliccin sa.

5. Sabon Allah ko aikata zunubi yana gusar da zaman lafiya a cikin al’ummah, kuma yana haifar da wahalhalu, kuma yakan haifar da tsadar rayuwa da tashin farashin kayayyaki, kuma yana rinjayar da mahukunta da makiya a kan mutane, kuma yana hana samuwar albarka da sauran su.

6. Siffofin halittar mutum kamar ido, harshe, kunne, hannu, farji, kafa da sauran su, duk suna cikin gurabun sabawa Allah da aikata zunubi, sai fa idan an ji tsoron Allah, an kiyaye su.

Babban Malami Imam Ibn Qayyim Al-Jauziyyah (Rahimahullah) yace:

“Karancin dacewa, lalacewar tunani, boyuwar gaskiya, lalacewar zuciya, dakushewar ambato, bata lokaci, gudun halittu, rashin tsoro tsakanin bawa da mahaliccinsa, rashin karbar addu’a, bushewar zuciya, shafewar albarka a cikin arziki da rayuwa, haramta samun ilmi mai albarka mai amfani, tufafin kaskanci, tozartawar makiya, kuncin zuciya, jarabtuwa da abokai na banza masu bata zuciya su bata lokaci, tsawaitar damuwa, rayuwa ta matsatsi da juyewar tunani, duk suna samuwa ne saboda sabon Allah, da aikata zunubi da shagala daga ambaton Allah, kamar yadda shuka take samuwa daga ruwa, da konuwa daga wuta, kishiyoyin wadannan abubuwa kuwa suna samuwa ne daga yiwa Allah da’a da biyayya.” [Duba littafin Al-fawa’id, 32-33]

Sannan babban Malami Sheikh Ibn Baz (Rahimahullah) Yace:

“Gaba dayan abun da yake cikin duniya da lahira na azaba da wahala da zafin radadi da sabubban su, duk abin da yake jawo su shine sabon Allah da zunubi, da sabawa umarnin sa, da yin watsi da hakkin sa (Allah).” [Duba Majmu’ al-Fatawa, 2/152]

Kuma babban Malami, Sheikh Ibn Al-Qayyim (Rahimahullah) ya sake cewa:

“Sabon Allah da barna suna wajabtar da damuwa da kunci da tsoro da bakin ciki da tashin hankali, da matsatsin zuciya da cututtukan zuciya, kuma basu da magani face tuba, koma wa ga Allah da istigfari (wato rokon gafarar Allah).” [Duba Zad al-Ma’ad, 4/191]

Kuma yazo cikin Majmu’ul Fatawa, 11/256 cewa:

“Duk wanda yayi zaton cewa zunubai ba za su cutar da wanda ya dage a kansu ba, to shi batacce ne, halakakke ne, sannan kuma ya sabawa Alkur’ani da Sunnah da Ijma’in Salaf (wato magabata) da limaman Muslunci.”

Ya ku jama’ah, lallai duk wanda ya samu kansa cikin sabon Allah to wajibi ne yayi kokari ya tuba, kuma tuba na gaskiya domin samun sa’idah da ingantacciyar rayuwa da haduwa da Allah cikin farin ciki mai dorewa. Kuma kada mutum ya zama mai fidda tsammani daga rahamar Allah, ya kasance yana mai ganin cewa ai zunuban sa sunyi yawan da Allah ba zai iya gafarta masa ba, a’a, Allah mai tausayin bayin sa ne, kuma mai yawan gafara ne, matukar anyi tuba na gaskiya. Lallai Allah yana gafartawa wanda yaso.

Abubakar As-siddiq (RA) Yace:

“Lallai Allah yana yafe manya-manyan laifuka, don haka kada ku debe tsammani, kuma yana azaba akan kananan laifuka, don haka kada ku rudu (da su).” [Duba Sharhu Sahihul Bukhari na lbn baddal, 19/267]

Aun Bn Abdullahi Bin Utbah yace:

“Luran bawa da zunuban sa suna sa ya bar zunubin, kuma nadamar bawa akan zunubin sa mabudine na tuba.” [Duba At-taubah na Ibn Abid Dunya, 138]

‘Yan uwa, ina rokon Allah ya gafarta muna dukkan zunuban mu, ya kuma dawwamar da mu a bisa hanya madaidaiciya, amin.

Ya ku ‘yan uwana ‘yan arewa, mu sani lallai al’amarin tsaro babban al’amari ne a rayuwar dan Adam, wanda idan an rasa shi, to komai ma zai yi wahalar samuwa. Sannan kuma babu abin da yake wahalar da hukumomi kamar sa.

Tabbas, wanda duk yasan abin da yake faruwa a yankin mu mai albarka na arewacin Najeriya na rashin tsaro, to yasan irin tashin hankali da fitinar da wannan al’ummah ta ke fuskanta, musamman Musulmin kasar nan da ‘yan arewa baki daya. Jama’ah, muna fama da masu satar mutane domin neman kudin fansa (kidnappers), muna fama da ‘yan fashi da makami, barayin shanu, ‘yan kungiyar ta’addan Boko Haram, ISWAF da sauran su. Muna fama da shaye-shaye a tsakanin matasa maza da mata, ga rikice-rikicen addini da na kabilanci, ga rikice-rikicen siyasa, ga matsalar talauci, ga matsalar rashin aikin yi, ga masifar jahilci, ga matsalar almajirci da dai sauran su.

Yau sama da shekaru goma kenan muke cikin wadannan fitintinu na rashin tsaro!!! Mutane da dama sun rasa rayukan su, wasu sun gudu, wasu sun rasa muhallan su, wasu sun rasa dukiyoyin su, iyalai da yawa sun tarwatse; uwa, uba da ‘ya’yan su duk sun tarwatse! Inna lillahi wa inna ilaihi raaji’uun…!!!

Wannan al’amari na rashin tsaro ya lakume rayukan manyan malamai, da jami’an tsaro da manyan mutane. Yanzu jama’ah ina mafita? Shin haka za mu zauna cikin wannan bala’i har sai ya game ko’ina, ko kuma ya gama lakume kowa da kowa?

Wal iyazu billah, ina rokon Allah ya Allah ka kawo muna dauki, amin.

‘Yan uwa na masu daraja, lallai, babu shakka sabon Allah da zunubi abu ne dake haifarwa da bawa matsaloli masu yawa a cikin rayuwar sa da kuma lahirar sa, amma kuma shi Allah mai yalwar falala ne, matukar mutum yayi nadama, ya gane kuskuren sa, kuma ya tuba, to lallai zai samu Allah mai yawan gafarta zunubai ne. Allah madaukakin Sarki yace:

“Ku tuba zuwa ga Allah gaba dayan ku yaku muminai ko kwa samu tsira da rabauta.”

Sannan ya sake cewa:

“Kace da su yaku bayin Allah wadanda suka aikata laifuka wa kawunan su kada ku debe zaton tunanin Allah ba zai iya yafe maku ba, lallai Allah yana gafarta zunubai gaba daya kuma shi Allah mai yawan gafara ne da jinkai ga bayin sa.”

Kalmar tuba tana da girma da dalilai masu zurfi, ba kamar yadda wasu da yawa daga cikin mu suke dauka ba, cewa kawai ka furta da harshe, amma kuma kaci gaba da aikata laifuka. Ka lura, ka kula da fadar Allah madaukakin Sarki:

“Ku nemi gafarar ubangijin ku sannan ku tuba zuwa gare shi.”

Zaka samu a wannan aya cewa shi tuba wani al’amari ne da yake karuwa ta hanyar neman gafarar ubangiji.

Kuma saboda duk wani babban al’amari zaka same shi yana da sharudda, saboda haka malamai suka ambaci sharuddan tuba, wadanda suka dauko daga cikin Alkur’ani da Hadisai kamar haka:

1. Barin aikata zunubi da gaggawa.

2. Yin dana-sani (nadama) akan abunda ka riga ka aikata na laifuka a baya.

3. Kudurta niyyar ba zaka sake komawa ga wannan laifi ba.

4. Mayar da hakkin wanda ka zalunta, ko barranta daga azzalumai, idan ya kasance kai ne ka ke taimaka masu.

Bayan wadannan kada mutum ya manta da wasu al’amurran na daban wadanda suna da muhimmanci kwarai wurin tabbatuwar tuba nagartacce, misali:

1. Ya zamanto don Allah mutum ya tuba daga zunubi, ba don wani abu ya bar laifin ba, ko don bashi da ikon aikata laifin, ko kuma ka bar zunubi don tsoron maganar mutane, sam ba tuba bane wanda yabar zunubi don kare mutuncin sa wurin mutane, ko don ba shi da iko, ko don kare lafiyar sa daga wata cuta da ake samu.

Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi, ya tausaya muna, ya yafe zunuban mu da laifukan mu, ya gyara yankin mu na arewa da Najeriya baki daya, amin.

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author