ADAMAWA: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban sakandare, darakta da ma’aikatacin kotu

0

Wasu dauke da makamai da ake zaton ‘yan bindiga ne, sun yi garkuwa da jami’in kotu, shugaban makarantar sakandare da kuma wani darakta a garin Sangare, kusa da Jami’ar Fasaha ta Modibbo Adama, Yola.

An bayyana sunan ma’aikacin kotun da aka yi garkuwa da shi Samuel Yaumande, wanda Daraktan Shigar da Kararrraki ne a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Adamawa.

Majiya daga iyalin sa, ta shaida cewa ’yan bindigar sun mamaye gidan sa a ranar Litinin da tsakar daren Litinin suka dauke shi da karfin bakin bindiga, suka tafi da shi.

Haka kuma wasu dalibai da ke zaune kusa da gidan suka shaida wakilin mu.

“Sun zo dauke da manyan bindigogi na zamani, suka rika yin harbi a sama, domin su firgita jama’a.

“Bayan sun yi harbe-harben su ne suka tafi da daraktan, da shugaban sakandare da kuma wasu mutane uku, wadanda daliban makaranta ne.

“Har zuwa yanzu dai ba mu kara jin komai daga wadanda aka yi garkuwa da su din ba, kuma ba mu ji daga wadanda suka yi garkuwar da su ba.”
Haka wata majiya ta shaida.

Da wakilin mu ya tuntubi kakakin yada labarai na ‘yan sandan Adamawa, Suleiman Nguroje, ya tabbatar da garkuwar da aka yi to amma ya bayar da adadin wadanda ya ce an yi garkuwa da su, ba daidai da yadda majiya ta tabbatar mana ba.

Nguroje ya ce “an shaida wa rundunar ‘yan sanda cewa an sace darakta da wasu mutane biyu.”

“Kuma tuni jami’an mu sun fantsama bincike da farautar wadanda suka yi garkuwar domin ceto wadanda ake yi garkuwar da su.”

Har yanzu dai ana ci gaba da yi wa mazauna kauyuka dauki-dai-dai, ana sace su tare da yin garkuwa da su.

Ko cikin makon jiya wani dan majalisar tarayya daga jihar Neja, ya bayyana cewa an bar Karamar Hukumar sa a hannun masu garkuwa da mutane sai kamun-kaji suke yi wa jama’a sun a garkuwa da su.

Share.

game da Author