Sakamakon bincike da aka yi ya nuna cewa likitoci za su iya amfani da na’urar gwajin cutar dajin dake kama nono wato ‘Mamograph’ domin gwajin cututtukan dake kama zuciya musamman ga mata.
Quan Minh Bui da sauran abokan aikinsa dake jami’ar California, San Diego ne suka gano haka inda suka kara da cewa na’urar na nuna yawan sinadarin ‘Calcium’ din dake nonon mace.
Bui yace yawan sinadarin ‘Calcium’ a nonon mace ne ki haddasa cututtukan dake kama zuciya kamar su hawan jini, bugawar zuciya, shanyewar bangaren jiki da sauran su.
Ya ce gano haka din da suka yi zai taimaka wajen kare mata daga kamuwa da wadannan cututtuka da wuri kafin yayi musu illa.
Cututtukan dake kama zuciya na daya daga cikin cututtukan dake cutar da kuma yin ajalin mata da dama a duniya.
A zamanin da ire-iren wadannan cututtuka kan kama manyan mutane ne wato wadanda suka tsufa. Sai dai yanzu abin ya canja domin da zarar mace ta fara haihuwa duk da kankantar shekaru za ta iya kamuwa da wadannan cututtuka.
A dalilin haka likitoci ke kira ga mata da su rika yawaita cin abincin dake kara karfin garkuwar jiki tare da yawan motsa jiki cewa yin haka zai kare su daga kamuwa da wadannan cututtuka sannan ya kara musu lafiya a jika.