KATSINA: ‘Yan bindiga ba su daina kai samame Jibiya ba

0

Alamomi na nuna cewa yarjejeniyar da gwamnatin Jihar Katsina ta kulla da masu garkuwa da mutane ba ta yi tasiri sosai ba.

Domin Rundunar ‘Yan Sandan Katsina ta tabbatar da wani samame da ‘yan bindiga suka kai a Jibiya, cikin Jihar Katsina, inda suka kashe mutum daya kuma suka arce da wata mata tare da jaririn ta mai shekara daya da haihuwa.

Kakakin rundunar Gambo Musa ya sanar da cewa mahara kimanin su 10 rufe da fuskoki sannan dauke da manyan bindigogi sun darkaki garin a kan babura, wajen 8 na dare, inda su na isa sai suka fara harbin kan mai tsautsayi, suka bindige mutum daya.

Wanda aka bindige din dai matashi ne mai kimanin shekaru 20, kuma ya mutu nan take.

“Daga nan sai suka darkaki gidan wani mutum mai suna Tasi’u Waliyyi, inda su na shiga gidan suka kwace wayoyin kowa, sannan kuma su ka umarci kowa ya kwanta kasa. Sun kuma karbe ‘yan kudaden da ke hannun su.”

Ya ce daga nan suka yi gaba da matar sa da kuma jariri mai shekara daya.

Mataimakin Sufurtanda na ‘Yan Sanda, Gambo Isah ya ce sun kuma zarce gidan wani mai suna Abu Abu, shi ma suka yi gaba da shi.

Ya kara da cewa amma jami’a ‘yan sandan Operation Puff Adder, Sojojin Operation Sharan Daji da kuma SARS na can su na kokarin ceto su.

Ko cikin makonni biyu da suka gabata, an yi garkuwa da iyalin wani malamin Babbar Kwalejin Kimiyya a Dutsinma, cikin Jihar Katsina.

Share.

game da Author