Hanyoyi 7 da mai fama da ciwon siga zai bi don kauce wa warin baki

0

Kungiyar likitocin hakora na Najeriya (NDA) ta hori duk masu fama da cutar siga wato (Diabetes) da su rika gaggauta zuwa asibiti a rika yi musu gwajin jini tare da ganin likitan hakora akai-akai cewa yin haka zai taimaka wajen kaucewa kamuwa da cututtukan da ake kamuwa da su a dalilin ciwon siga.

Wadannan cututtuka kuwa sun hada da cututtukan dake kama baki musamman warin baki, makanta, hawan jini, rashin karfin kashi, ciwon koda, shanyewar bangaren jiki, rashin warkewar rauni da dai sauran wasu cututtukan.

A dalilin haka suke kira ga masu dauke da wannan ciwo da su rika tsaftace kowani bangare na jikinsu musamman bakunan su sannan su yawaita zuwa asibiti domin ganin likita.

Likitocin sun kuma bada wasu hanyoyi 7 da za su taimaka wajen guje wa haka

1. Zuwa asibiti domin yin gwajin jini sannan da ganin likitan hakora.

2. A daina yin amfani da magogin baki mai karfi wajen wanke baki sannan a rika kuskure baki akai a kai da ruwan kuskure baki da aka inganta wato ‘Mouth Wash’

3. Za a iya yin amfani da mankade a fata domin warkar da rauni a jiki.

4. A yawaita cin kayan lambu kamar su lemu,ayaba da ganyayyaki.

5. A rika shan magungunan da likita ya bada a lokacin da ya kamata.

6. A kauracewa shan giya da kuma busa taba sigari.

7. A rika tsaftace jiki akai akai.

Ciwon siga na kama mutum ne idan aka samu matsala da wasu daga cikin ababen da ke sarrafa abincin da muke ci a cikin mu.

Insulin na aiki ne a jiki wajen tace sinadarin ‘Carbonhydrate’ dake cikin abincin da muke ci don samar wa mutum kuzarin da yake bukata a jiki.

A dalilin rashin aikin ‘Insulin’ yadda ya kamata ne ya ke sa a kamu da ciwon siga.

Sakamakon binciken majalisar dinkin duniya ya nuna cewa cutar ta yi ajalin mutane miliyan 1.6 a duniya.

Majalisar ta ce domin rage yaduwar wannan cuta za ta yi amfani da watan Nuwanba ta kowace shekara domin wayar da kan mutane ilolli da hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.

Share.

game da Author