KANJAMAU: Har yanzu cutar na ci gaba da yaduwa a Najeriya – Hukumar NACA

0

Shugaban hukumar hana yaduwar cutar Kanjamau ta kasa (NACA) Gambo Aliyu ya ce adadin yawan mutanen dake kamuwa da Kanjamau da adadin yawan dake mutuwa a dalilin cutar a Najeriya sun kai rabin yawan da duniya ke fama da.

Aliyu ya fadi haka ne a taron shirin ranar cutar Kanjamau ta duniya da kungiyar ta yi a Abuja.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta kebe ranar daya ga watan Disemba na kowace shekara domin wayar da kan mutane game da kanjamau.

Taken taron a bana shine ‘Karkato da hankulan mutane domin samar da mafita game yaduwar cutar’.

Aliyu ya ce taron a bana zai fi maida hankali ne wajen karkato da hankalin mutane kan rawan da za su iya takawa wajen dakile yaduwar cutar saboda bincike ya nuna cewa kashi 60 bisa 100 na mutane basu da masaniya game da cutar a kasar nan.

Shugaban kwamitin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na majalisar dattawa Chukwuka Utazi ya ce burin gwamnati shine ta ga ta hada hannu da mutane da ‘yan siyasar kasar nan domin ganin an samu nasarar kawar da cutar.

Bayan haka Aliyu ya kuma jadadda cewa babu maganin kawar da cutar kanjamau illa maganin dake hana yaduwar ta.

Ya ce a dalilin haka yake kira ga mutane da su yi watsi da zancen gano maganin warkar da cutar da wasu ke ta yadawa.

“ Akwai wani likita mai suna Jeremiah Abalaka da ya fito yana shirga wa mutane karya wai yana da maganin warkar da cutar kanjamau.

“ Abalaka karya kawai yake kantara wa mutane domin a shekarun da suka gabata mun aika da mutane 30 domin Abalaka ya warkar da su amma ya kashe 29 daya kawai ya rayu.

Idan ba a manta ba a watan Maris din da ya gabata ne hukumar NACA ta gabatar da sakamakon binciken adadin yawan mutanen dake dauke da kanjamau a Najeriya.

Sakamakon ya nuna cewa mutane miliyan 1.9 ne ke dauke da cutar sannan matasa masu shekaru 15 zuwa 49 ne suka fi yawan kamuwa da cutar.

Binciken ya muna cewa mutane kashi 42.3 ne ke samun maganin cutar a kasar nan.

Share.

game da Author