SOKE ALAWUS: Kungiyar CISLAC ta jinjina wa Majalisar Jihar Zamfara

0

Kungiyar Rajin Kare Marasa Galihu da Dimokradiyya, watau CISLAC, ta cira wa Majalisar Jihar Zamfara hula, bisa ga hobbasa da namijin kokarin da ta yi wajen soke dokar bai wa tsoffin gwamnoni da mataimakan su makudan kudade bayan sauka daga mulki.

Dokar dai wadda Majalisar Jihar Zamfara ta soke, ta ce aka rika amfani ana biyan tsoffin gwamnoni, mataimakan su, tsoffin shugabannin majalisar dokokin jiha da mataimakin makudan kudade.

Soke dpkar ya biyo bayan fallasa wata wasika da aka yi, wacce tsohon gwamna, Abdul’aziz Yari ya rubuta wa Gwamna Bello Matawalle wasikar tunatar da shi a biya shi na sa kudaden.

Kwana uku bayan fitar wasikar sai Majalisar Dokokin Zamfara ta yi zama uku a rana daya, inda ta rattaba soke dokar.

A kan haka ne CISLAC ta hannun Babban Daraktan kungiyar, Auwal Rafsanjani, ya fitar da takardar nuna yabo ga majalisar ta jihar Zamfara.

Ya kuma roki sauran majalisun sauran jihohi su yi koyi da ta Zamfara, su soke wadannan dokoki da ake kirkirowa domin ci gaba da wawuran makudan kudaden ya suka kamata a yi wa al’umma aiki da su.

Rafsanjani ya kuma yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari, ya tsaya ya tabbatar cewa gwamnoni da majalisun su rika tsayawa ga karbar kudaden da Dokar RMFAC ta amince su karba kawai.

“Abin takaice a wannan hali da ake ciki, wasu tsoffin gwamnoni su rika kwashe kudaden jama’a da sunan fansho ko sallama ko. Abin haushi har doka su je kafawa cewa idan sun sauka a gina musu gida, kuma a rika ba su fansho har karshen rayuwar su. Inji CISLAC.

Share.

game da Author