A wani abu mai kama da nade tabarmar kunya, Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya yi kokarin kare dalilin da ya sa ya sa hannun neman Najeriya ta biya wani kamfanin wasu lauyoyin kasar Turai, mai suna Trobell Limited.
Shugaba Muhammadu Buhari ne ya aika wa Malami wasika ta hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari.
Wasikar na dauke da sakon cewa Buhari ya umarci Malami ya gaggauta soke waccan yarjejeniya da aka yi da Trobell Limited, bisa dalilin cewa kudaden da Malami ya rubuta za a biya kamfanin, sun yi yawan da ya zarce tunanin duk wani mai hankali.
Sannan kuma Buhari ya ce ko babu wannan kamfanin ejan na lauyoyi, to Najeriya za ta iya karbar kudaden ta daga kamfanonin hakar danyen mai na duniya.
Kusan dala biliyan 62 ce Najeriya ke nema daga wannan manyan kamfanoni. Amma Kotun Kolin Najeriya ta kayyade musu biyan dala bilyan 43.
A kan haka ne Buhari ya ce ai tunda har Kotun Kotun Koli ta ce tilas su biya, to sai fa sun biya, ko ejan din da Malami ya kawo ba su shiga tsakani ba.
Kudaden da Malami ya so a biya ejan Trobell Limited, sun kai naira bilyan 774, kwatankwacin dala bilyan 2.15 kenan.
Sai shi kuma Malami, a cikin wata wasika da ya aika wa Abba Kyari, ya bayyana wa Shugaba Buhari cewa ai kudin ma da ya nemi a bai wa ejan din kashi 5 bisa 100, cikin cokali ne, idan aka kwatanta da abin da gwamnatin baya ta rika bayarwa idan ejan ya taya ta karbar kudaden ta daga waje.
Ya buga misali da yadda gwamnatin Goodluck Jonathan ta biya har kashi 30 bisa 100 na wasu kudade da wani ejan ya taya gwamnatin karbowa.
A yanzu dai za a iya cewa an rufe shafin biyan wadannan makudan kudade.
Dama kuma an rika yin zarfin cewa kamfanin na wasu abokan Malami ne.