Bankin Habbaka Tattalin Arzikin Afrika ya nemi a kara samar wa matan Afrika tallafin kudade

0

Bankin Habbaka Tattalin Arzikin Afrika, watau African Development Bank (AfDB) ya yi kira da a gaggauta samo hanyoyin da matan Afrika za au kara samun kudade masu yawa, domin inganta tattalin arzikin Nahiyar.

Shugaban AfDB, Akinwumi Adesina ne ya yi wannan kiran, a lokacin da ya ke jawabi wurin taron Gano Hanyoyin da ke kawo cikas wajen samar da daidaito tsakanin maza da mata.

An gudanar da wannan kasaitaccen taro a Kigali, babban birnin kasar Kigali, daga ranar 25 zuwa 27 Ga Nuwamba.

Manyan bankuna na duniya tare da AfDB da Gwamnatin Rwanda ne suka shirya taron, domin gano hanyar da za a kara yawan kudaden tallafi da lamunin da cibiyoyin hada-hadar ke raba wa mata.

Akinwumi ya ci gaba da cewa, “Nauyin cibiyoyin hada-hadar kudade da ke Afrika su tashi haikan wajen ganin sun kara wa mata yawan lamunin kudaden da su ke raba wa mata.

” Baya ga cewa maza sun fi karbar wannan lamuni daga bankuna, amma abin mamaki, kashi 90 na mata bincike ya nuna cewa ba su da taurun bashi.

Don haka ya ce bai ga wani dalilin za zai sa masu bankuna su rika yin shakkun dankara wa mata bashi ba, tunda dai su na biya.

Shugaban na AfDB ya ce daga yanzu za su rika aunawa da nazarin irin tallafin da bankunan Afrika ke bai wa mata.

A jawabin ta, Ministar Harkokin Mata ta Senagal, Salimatu Diop Deng, ta ce wannan aiki ne babba wanda sai an tallafa wa matan Afrika sosai domin kara inganta tattalin arziki.

Share.

game da Author