Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya gabatar da Naira biliyan 249.5 a matsayin kasafin kudin shekarar 2020 na jihar.
Ya gabatar da kasafin ne a majalisar dokokin jihar ranar Laraba yana mai cewa kasafin 2020 zai fi bada karfi ne wajen samar da ayyukan ci gaba a jihar.
Bisa ga kasafin gwamnati ta ware Naira biliyan 75.6 a matsayin kudaden da za a kashe na ayyukan yau da kullum sannan Naira biliyan 173.9 a matsayin kudaden da za a kashe kan manyan ayyuka a jihar.
Masari yace an samu karin Naira biliyan 48.7 a kasafin kudin shekarar 2020 saboda karin kudaden shiga da
da aka samu.
“ Hakan ya sa jimlar kudaden da gwamnati zata kashe na yau da kulun a kasafin ya karu da kashi 23.72.
Bayan nan ya yaba wa mutanen jihar bisa zaben APC da suka yi a zaben 2019 da kuma ci gaba da mata wa jam’iyyar baya a jihar.
A karshe kakakin majalisar Tasiu Maigari yace nan bada dadewa ba majalisar za ta gayyaci duk ma’aikatun dake jihar domin yin bayani game da kasafin kudin ma’aikatar su..