Kotu ta jaddada nasarar Gwamna Mutawalle na Zamfara

0

Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Gwamnoni a Abuja, ta kori karar da aka shigar domin neman kotun ta sauke Gwamna Bello Mutawalle na Jihar Zamfara.

Dan takarar jam’iyyar APDA, Muhammed Takori ne ya shigar da Mutawalle na PDP kara tare da hadawa da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ya maka kotu.

Takori da jam’iyyar APDA sun nemi kotu ta soke nasarar da Kotun Koli ta bai wa Mutawalle, bisa hujjar cewa gwamnan bai samu kuri’u kashi biyu bisa uku na adadin wadanda aka jefa a kananan hukumomin jihar ba, kamar yadda dokar zabe ta kasar nan ta rattaba.

Sannan kuma masu kai kara sun yi inkarin yawan kuri’in da INEC ta ce sunn lalace a ranar da aka jefa kuri’a a zaben gwamnan, na jihar Zamfara.

Sai dai kuma a lokacin da ta ke yanke hunci, Mai Shari’a Binta Zubair ta ce wannan kara da APDA ta shigar ba ta da wani tushe ballantana makama, domin Kotun Koli ta rigaya ta yanke hukunci a ranar 24 Ga Mayu, 2019.

Don haka Binta a madadin ita kan ta da sauran alkalan, ta ce kuri’un da aka jefa wa Mutawalle da PDP a Jihar sun tabbata wadanda dokar kasa ta amince da su, a zaben gwamnan Jihar Zamfara da aka gudanar a ranar 9 Ga Maris, 2019.

Sannan kuma kotun ta ki amincewa da inkarin da masu kara suka yi cewa Mutawalle bai samu kuri’u kashi biyu bisa uku a kananan hukumomin jihar ba.

Tun da farko dama kuma kotun ta yi watsi da korafin da masu kara suka bayar cewa jam’iyyar PDP ba ta gudanar da zaben fidda-gwani a jihar Zamfara ba, don haka Mutawalle bai cancanci tsayawa takara ba.

Kotun ta ce batun zaben fidda-gwani magana ce ta cikin gidan jam’iyya, kuma batu ne da ya kamata a duba a kotu tun kafin a yi zabe, ba sai bayan an gudanar da zabe ba, wanda wannan Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Gwamna ce, ba ta sauraren kararrakin zaben fidda-gwanin jam’iyyu ba ce.

Bayan yin watsi dackarar da kotu ta yi, ta kuma umarci masu karar su biya Mutawalle naira 500,000 ladar wahalar bata masa lokaci da suka yi a kotu.

Share.

game da Author