RUFE KAN IYAKOKI: Aljifan manoman shinkafa sai cika su ke fal da makudan kudade – Minista

0

Sakamakon rufe kan iyakokin Najeriya, hakan ya zaburar da noman shinkafa ya inganta a kasar nan, yadda a yanzu manoman shinkafa sai samunn albarkar makudan kudaden shinkafar da suke nomawa suke yi.

Karamin Ministan Harkokin Noma da Inganta Karkara, Mustapha Shehuri ne ya bayyana haka Wata sanarwa da aka turo wa PREMIUM TIMES, ta tabbatar da cewa Shehuri ya yi wannan bayani a wani Gidan Kiwon Dabbobi mallakar ma’aikatar gona ta tarayya da ke a Mando, Jihar Kaduna, a ranar Asabar da ta gabata.

“Sai kudade suke samu, su na ta garzayawa bankuna su na ajiya, saboda ana ci gaba da samun cinikin shinkafar mu da ake nomawa a nan cikin kasa. Hakan kuwa zai kara samar da ayyuka ga matasa da kuma karfafa harkokin noma da kiwo da sauran harkokin masarufi daban-daban.” Inji Minista Shehuri.

Baya ga rufe kan iyakokin da ministan ya ce ya taimaka an karkato wajen cinikayyar shinkafar da ake nomawa a nan cikin Najeriya, Shehuri ya kara da cewa tsare-tsaren bayar da tallafi da gwamnatin tarayya ke bai wa manoma ya kara inganta da karfafa noman shinkafa da sauran nau’o’in kayan abinci a cikin kasar nan.

Shehuri ya ce gwamnatin tarayya za ta raba wa kananan manoma kayan aikin gona yadda za a kara karfafa musu guiwa sosai.

PREMIUM TIMES ta bayar da rahoton cewa duk da kalubalen da ake fuskanta wajen bayar da tallafin lamunin noma na ‘Anchor Borrowers’ da Babban Bankin Najeriya, CBN ke bayarwa, tsarin ya karfafa noma sosai a Najeriya.

MANOMAN SHINKAFA: MURNA ZA TA KOMA CIKI?

Sai dai kuma kwanaki biyu rak bayan da Karamin Ministan Gona Shehuri ya yi wannan bayani na yadda manoman shinkafa ke ci gaba da girbar makudan kudaden ribar noman su, shi kuma Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu cewa ya yi nan gaba kan farashin shinkafar da ake nomawa a nan cikin kasar nan zai fadi kasa warwas.

Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, ya bayyana cewa albarkar da aka samu a fannin noma shinkafa a wannan daminar zai taimaka kwarai wajen karyar da farashin shinkafa, ta yi arha takyaf.

Bagudu wanda shi ne Shugaba Kwamitin Shugaban Kasa na Noman Shinkafa da Alkama, ya yi wannan jawabi ne a yau Litinin a garin Argungu, jihar Kebbi, a lokacin da ya ke taron ganawa da manoman shinkafa na yankin.

“Albarkar noman da aka samu a wannan damina zai rage tsadar shinkafar da mu ke nomawa a nan gida, kuma hakan zai kara rage bukatar shigo da ta fasa-kwauri a cikin kasar nan. Sannan kuma ta nan gida za ta yi arhar da duk irin talaucin mutum ba zai kasa sayen ta ba.” Inji Bagudu.

Bagudu ya kuma shaida wa manonan cewa gwamnatin sa nan ba da dadewa ba za ta shigo da kananan injinan casar shinkafa ta raba su manoman domin karfafa ingancin shinkafar da manoman ke cashewa su na kai wa kasuwanni.

“Tuni dai an rigaya an horas da matasa yadda za su rika sarrafa wadannan injina da za mu raba a dukkan kananan hukumomi 21 na wannan jihar.” Inji Bagudu a wurin taron.

Mawi manomi mai suna Abubakar Usman, ya shaida wa gwamna cewa sun samu shinkafa mai tarin yawa a bana, kuma su na so a shekara mai zuwa ma albarakar noman ta su ta wuce wadda suka samu a bana.

Sai dai kuma ya roki gwamna cewa gwamnatinin jihar Kebbi ta tallafa musu da takin zamani, maganin kashe kwari da kuma injinan casar shinkafa.

Share.

game da Author