Yadda mahara suka fatattaki mazauna kauyuka 17 a jihar Kaduna

0

Mahara sun fatattaki mazaunan kauyuka 17 a karamar hukumar Igabi a
dake jihar Kaduna.

Wannan abin tashin hankali da tsoro ya auku ne ranar Lahadin mako da ya gabata.

A yanzu haka wadannan mutane suna zaman gudun hijra a makarantar firamaren dake kauyen Birnin Yero.

Mai unguwar kauyen Unguwar Gibe, Jibrin Abdullahi ya bayyana cewa maharan sun dade suna kai wa mazauna wadannan kauyuka hare-hare inda hakan ya sa ‘yan bangan kauyukan suka hadu domin afkawa maharan a maboyan su.

Abdullahi yace maharan sun fatattaki mutane 2000 daga kauyukan Tura, Unguwan Gebi, Unguwan Dangauta, Unguwan Nayawu, Unguwan Makeri, Jagani, Sabon Gida, Dallatu, Unguwan Alhaji Ahmadu, Sabon Gari, Kusau, Gidan Sarkin Noma, Unguwan Pati, Unguwan Tofa da Sauran Giwa

Limamin masallacin Izala Ibrahim Usman ya gargadi mutane da kada su rika karya doka, kamar yadda wasu matasa suka yi kokarin datse Titin Zariya zuwa Kaduna a dalilin haka.

Ya kuma kara yin kira ga gwamnatin Kaduna da ta gaggauta kawo musu dauki a kauyukan su.

Mai unguar kauyen Birnin Yero Umar Danyaro da Dagacen Rigachukun Abdulraheed Sani sun yi kira ga mutane da su kara hakuri cewa gwamnati za ta dauki mataki domin magance matsalar.

Bayanai sun nuna cewa ma’aikatan hukumar bada agajiin gaggawa ta kawo wa karamar hukumar ziyarar gani wa kanta abubuwan da suka auku.

Share.

game da Author