A taron da akayi don tattauna hanyoyin da za a bi wajen dakile yaduwar cutar tarin fuka, kanjamau da zazzabin cizon sauro da asusun duniya ta shirya a Lyon kasar Faransa gwamnatin Najeriya ta yi alkawarin bada da gudunmawar dala miliyan 12 domin kawar da wadannan cututtuka a duniya.
An shirya wannan taro ne domin tattauna yadda za a tara kudaden da za a ayi amfani da su wajen hana yaduwar wadannan cututtuka a duniya nan da shekaran 2030.
A wani takarda da aka raba wa manema labarai, jami’in hulda da jama’a na hukumar hana yaduwar cutar kanjamau ta kasa (NACA) Toyin Aderibigbe ya sanar da haka yana mai cewa asusun duniya na sa ran tara akalla dalla biliyan 14.02 nan da shekaru uku daga gudunmawar da kasashen duniya za su bada.
Aderibigbe ya ce asusun duniya za ta yi amfani da wadannan kudade ne domin ceto rayukan mutane miliyan 16 a duniya daga nan zuwa 2030.
Bayan haka ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya shaida cewa gwamnatin Najeriya na iya kokarinta wajen ganin ta kara ware wa fannin kiwon lafiyar kasar kudade masu tsoka domin samar wa mutane kariya daga kamuwa da wadannan cututtuka.
Shugaban UNAIDS Gunilla Carlsson ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta hada kudaden tallafin da take samu da wadanda take warewa domin inganta kiwon lafiyar kasar.
Discussion about this post