TARIN FUKA: Najeriya da wasu kasashe na cikin hadarin gaske

0

Sakamakon binciken da Kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya (WHO) ya nuna cewa Najeriya da wasu kasashen Afrika guda bakwai ba su iya maida hankali ba wajen dakile yaduwar tarin fuka a kasashen su.

Wadannan kasashe sun hada da India, China, Indonesia, Philippines, Pakistan, Nigeria, Bangladesh da Africa ta kudu

Rahotan ya nuna cewa cutar kara yaduwa a wadannan kasashe inda a yanzu haka wasu mutane sabbi da suka kai kashi 66 bisa 100 sun kamu da cutar a wadannan kasashe

Najeriya za ta iya dakile yaduwar wannan cuta ne idan ta daina yawan dogaro da tallafin da take samu daga kasashen waje, ta shirya hanyoyin samar isassun magunguna, karo ma’aikata tare da horas da su kan yadda za su iya gano cutar da wuri.

Idan ba a manta ba bincike ya nuna cewa mutane miliyan 10 sun kamu da tarin fuka a duniya a shekaran 2018.

Daga cikin wannan yawa maza sun kai miliyan 3.2,mata da yara kanana miliyan 1.1 sannan masu dauke da cutar kanjamau sun kai kashi 9 bisa 100.

Bayan haka binciken ya nuna cewa an samu ragowar yawan mace-macen mutanen dake dauke da wannan cuta a shekaran 2018. Domin a 2018 mutane miliyan 1.5 ne suka rasu sannan a 2017 mutane miliyan 1.6.

Hakan na da nassaba ne da yadda asusun hana yaduwar cutar da sauran kungiyoyin bata tallafi suka zage damtse wajen kula da mutane miliyan bakwai dake dauke da cutar.

Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus yace nan ba da dadewa ba kasashen dake tasowa da sauran kasashen duniya za su samu kawar da cutar.

Share.

game da Author