Sai an kara narka wa sojoji kudi sannan za su iya dakile Boko Haram -Inji Buratai

0

Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Janar Tukur Buratai, ya bayyana cewa sai an kara wa fannin tsaro na sojoji makudan kudade, kafin su iya magance Boko Haram da sauran matsalolin tsaro a kasar nan.

Buratai ya ce tabbas kudaden da ake ware wa tsaro sun yi kadan, idan aka yi la’akari da irin kalubalen da sojoji ke fuskanta.

Ya yi wannan kira ne a lokacin da ya ke jawabi wurin Taron Bitar Tsantsenin Kashe Kudaden Sojoji, karo na 12, a Uyo, babban birnin Jihar Akwai -Ibom, a jiya Litinin.

Buratai ya ce akwai gagarimin kalubale a hannun sojoji, idan aka yi la’akari da matsalolin tsaro a kasar nan. Amma duk da rashin wadatar kudade, Buratai ya ce sojoji sun taka muhimmiyar rawa, kuma su na kan takawa har yanzu, wajen tabbatar da tsaro a fadin kasar nan.

Buratai, wanda Babban Kwamandan Runduna ta 6, Manjo Janar Jamil Sargham ya wakilta, ya kara da cewa shigo da ke tsarin Asusun Bai-daya na TSA, tsarin biyan albashi na keke-da-keke, wato IPPIS da kuma tsarin daina kinkimar makudan kudade, wato ‘cashless policy’, sun taimaka an toshe kofofin da kudade ke zurarewa a fannin tasarifin kudade a karkashin jami’an sojoji.

Ya ce sojojin Najeriya za su ci gaba da biyayya ga gwamnatin dimokradiyya ba tare da gajiyawa ba.

A na sa jawabin, shi ma Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ita kadai ba za ta iya daukar dukkan dawainiyar ayyukan tsaron da sojoji ke gudanarwa a kasar nan ba.

Share.

game da Author