Gwamnonin kasar nan 36 sun tsokano wata sabuwar kwatagwangwamar biyan albashi, inda su ka bayyana cewa ba za su bi sabuwar yarjejeniyar da Gwamnatin Tarayya ta cimma tare da Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC ba.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi ne ya bayyana haka a Abuja, jim kadan bayan tashi daga wani taro da gwamnonin suka yi.
An gudanar da taron a otal din Hilton, kuma dukkan hwamnonin sun halarta.
Da ya ke jawabi a madadin sauran, Gwamna Fayemi ya ce Tarayya daban, haka kuma jihohi daban. Don haka za su koma su yi ta su mai fisshe su a kowace jiha, domin tattauna adadin da za su iya kara wa ma’aikata albashi.
Sai dai kawai ya ce gwamnoni sun amimce cewa mafi kankantar albashi ba zai yi kasa da naira 30,000, ga masu matakin albashi na 01 zuwa 06, kamar yadda sabuwar doka ta gindaya.
Amma daga mataki na 07 abin da ya kai na 17, to na za su iya yin karin kusan kashi 60 bisa 100 ba, sai dai su yi kintace su dan kara musu abin da ya saukaka kawai.
Gwamnatin Tarayya dai ta cimma cewa za ta yi karin kashi 20 bisa 100 ga masu 07 zuwa 08, sai kashi 19 ga masu 09, sai kuma kashi 16 ga masu 10 har zuwa 14.
Masu matakin albashi na 15 zuwa 17 ne aka amince za a yi wa karin kashi 14 bisa 100.