Mai Shari’a Akon Abang na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya bada umarnin a tsare tsohon Shugaban Kwamitin Tsaftace Fansho, Abdulrashid Maina a kurkuku.
Maina dai ana zargin sa ko tuhumar sa da aikata laifuka 12, wadanda suka hada da harkallar kudade, asusun ajiyar bankuna birjik na bige da kuma zamba.
Sannan kuma duk a rana daya kuma a kotu daya, sannan mai shari’a daya, wato Abang, ya bada umarnin a ci gaba da tsare dan Maina mai suna Faisal a hannun Ofishin ‘Yan Sanda na Asokoro, Abuja, har zuwa ranar 6 Ga Nuwamba.
Ana tuhumar Faisal daclaifin harkalla ta hanyar karkatar da kudade a wani asusun sa da ke bankin UBA.
Daga cikin kudaden da ake tuhumar sa, har da wata naira milyan 58 da EFCC ta shaida wa kotu.
Shi kuma mahaifin sa Maina ana tuhumar sa da wawure kudaden da aka ce sun kai naira bilyan 100.
Za a ci gaba da shari’ar Maina a ranar 30 Ga Oktoba. An bada umarnin tsare shi, kwanaki biyu bayan da wata Babbar Kotun Tarayya a karkashin Mai Shari’a Folashade Ogunbanjo ta bada umarnin EFCC ta rike wasu kadarorin sa, wadanda yawanci gidaje ne, har guda 23.
Cikin 2013 ne gwamnatin Goodluck Jonathan ta kori Maina daga aiki, kuma ya gudu ya bar kasar.
Gwamnatin Buhari ta yi sunkurun dawo da shi aiki ta karkashin kasa a cikin 2017. Amma daga baya an fallasa al’amarin, wanda ya zubar wa gwamnatin kimar da ake gani ta na da ita, musamman bangaren yaki da cin hanci da rashawa.