Masu garkuwa sun saki dalibai da malaman makarantan Kaduna

0

Da safiyar Asabar ne ‘yan mata shida da malamai biyu da aka yi garkuwa da su a wani makaranta mai zaman kansa a Kaduna suka kubuta daga tsarewar masu garkuwa.

An sako wadannan dalibai da malaman su ne ranar Asabar da sassafe.

Iyayen daya daga cikin daliban da aka yi garkuwa da su ta bayyana cewa a mahadar makarantar Command dake Kaduna ne suka je suka dauko yaran na su.

Idan ba a manta ba makonni uku da suka wuce ne mahara suka yi garkuwa da wasu ‘yan mata shida da malamai 2 a wani makarantar kwana mai suna (Engravers College) da ke unguwar Sabon Tasha a Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya yi kira ga mutane da su rika taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri domin cafke batagari dake addabar mutane a jihar.

Share.

game da Author