A ranar Talata ne kotun Majistare dake jihar Kano ta gurfanar da wani malamin kwalejin kimiyya da Fasaha dake Kano, Ali Shehu mai shekaru 36 a bisa laifin yin lalata da wata dalibar sa.
Alkalin kotun Muhammad Idris ya yanke hukuncin a ci gaba da tsare Shehu a kurkuku sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 15 ga watan Oktoba.
Dan sandan da ya shigar da karar, Badamasi Gawuna ya bayyana cewa Shehu ya yi kokarin danne dalibarsa ne a ranar 19 ga watan Agusta da karfe 11 na safe.
Gawuna yace a wannan rana Shehu ya dauki wannan dalibar ya kai ta Ummi Plaza dake garin Kano domin ta taya shi tattance jarabawar dalibai inda a nan ne ya yi kokarin danne ta.
“Dalibar ta bayyana cewa Shehu ya saka hannun sa a gabanta sannan yayi kokarin danne ta.
Shehu dai ya amsa laifin da ya aikata a kotun.
Idan ba a manta ba a ranar Litini ne BBC ta saki wani bidiyon yadda wani babban malamin Jami’ar Legas Boniface Igbeneghu ya yi kokarin yin lalata da wata yarinya da ta je wajen sa a matsayin mai neman a dauke ta shiga jami’ar.
Kiki Mordi dake aiki da jaridar BBC Africa ta dauki bidiyon yadda wannan malami ya yi kokarin yin lalata da ita a cikin ofishinsa duk ba tare da sanin malamin ba wato Igbeneghu.