Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin naira tiriliyan 9.75 da aka yi hasashen kashewa a shekara mai zuwa, ta 2020.
Da ya ke jawabi a karon farko a zauren sabuwar zubin Majalisa, Buhari ya ce an yi kintacen samun riba ta naira tiriliyan 2.64 daga albarkatun man fetur, sai kuma naira tiriliyan 1.81 daga fannonin da ba fetur da dangogin sa ba.
Buhari ya ce za a kashe naira tiriliyan 2.45 wajen biyan basussuka na cikin gida da na waje.
An ware wa harkokin tsaro naira bilyan 110, yayin da aka ware naira bilyan 37.83 wajen shirin Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas.
Buhari ya ce an samu cikas a kasafin 2019, saboda jinkirin da aka yi kafin a amince da kasafin da kuma rashin tara makudan kudaden harajin da aka yi kintacen tarawa a 2018.
Buhari ya ce an yi hasaahen samun kidaden shiga har naira tiriliyan 8.155 da Gwamnatin Tarayya ke sa ran tarawa gabadaya.
Baya ha kudaden shiga na ferur da wadanda ba na fetur ba, akwai kuma kudaden shiga da ake sa ran samu daga sauran bangarori har naira tiriliyan 3.710.
An samu gibin maira tiriliyan 2.18 a Kasafin 2020
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana samun gibi a Kasafin 2020 da ya gabatar yau a Majalisa, har na naira tiriliyan 2.18.
Da ya ke jawabi, Buhari ya ce sai dai kuma gibin bai kai kashi 3% da dokar kasafin kudi ta ce ba ta yarda a samu ba.
Buhari ya ce za a cike wannan wawakeken gibi da basussukan da za a ciwo a nan cikin gida da kuma waje.
Biyan Bashi
Dangane da ci gaba da biyan basussuka da Najeriya ke yi, Buhari ya ce za a biya har naira tiriliyan 2.45 a cikin kasafin 2020. Sannan kuma ya ce gwamnatin tarayya za ta bada karfi wajen ramcen kudade daga tsarin Sukuk, Green Bonds da Diaspora Bonds.
Da ya waiwaya kan kasafin 2019 da ya gabata, Buhari ya ce an samu nasarar rage hauhawar farashi da tsadar rayuwa daga kashi 18.17 cikin 2017, zuwa 11.02 a karshen Agusta, 2019.
Ya kuma bugi kirjin cewa asusun ajiyar dukiyar Najeriya a waje ya karu daga dala bilyan 23 cikin 2016 zuwa dala bilyan 42.5 cikin Augusta, 2019.
Harajin VAT
Buhari ya ce an kara harajin VAT daga kashi 5% zuwa 7.5% domin a yi amfani da kudaden wajen inganta lafiya, ilmi, kayan more rayuwa, inda jihohi da kananan hukumomi za su rika kwasar kaso 85% na kudaden.
Buhari ya ce ba za a karbi harajin VAT daga magunguna, littattafai, kayan masarufi da sauran su ba.