A babban birnin tarayyan Najeriya Abuja wasu mahara suka far wa mutane inda suka arce da mutane tara sannan suka harbi wani ma’aikacin hukumar NSCDC a wannan farmakin da suka kai.
Wannan abin tashin hankali ya auku ne a hanyar Peki ranar Litini da yamma.
Kakakin rundunar Sintirin na ‘Civil Defence’ (NSCDC) Emmanuel Okeh ya bayyana cewa Tosin Ayeni dake aiki da rundunar na daga cikin mutane tara da aka yi garkuwa da su sannan Aku Atta ma’aikacin rundunar wanda maharan suka harba na samun kula a asibiti.
Bayan haka rundunar ‘yan sandan Abuja a wani takarda da ta raba wa manema labarai ranar Talata da yamma ta tabbatar da aukuwar haka sai dai rundunar bata fadi adadin yawan mutanen da aka yi garkuwa da su ba.
Sannan ta tabbatar da cewa tana iya kokarinta domin ganin ta ceto mutane tara da maharan suka yi garkuwa da.
A yanzu haka wadannan maharan sun kira iyalen mutanen da suka sace din inda suka bukaci a biya su kudin fansa.
Yin garkuwa da mutane domin karban kudaden fansa ya zama ruwan dare a Najeriya sai dai kuma rundunar ‘yan sanda a Abuja ta ce ta ayyukan mahara da masu garkuwa ya rag matuka a Abuja da kuma kasa baki daya.