Wani kwararren likitan kwakwalwa dake aiki a asibitin masu fama da matsalar tabuwar hankali a Yaba jihar Legas Abdur-Rasheed Awesu ya yi kira ga gwamnati, masu ruwa da tsaki da ma’aikatan kiwon lafiya da su wayar da kan mutane game da illolin dake tattare da samun matsala a kwakwalwar mutum yana mai yin gargadi da arika wayar wa mutane kai akai akai.
Awesu ya ce yin irin wannan kira ya zama dole ganin cewa matsalar kisan kai na neman ya zama ruwan dare a kasar nan.
Ya ce mutum kan samu matsalar tabuwar hankali ne idan an samu matsala a yadda yake tunani ko kuma yadda yake ganin abu a rayuwa.
Idan ba a manta ba a watan Satumba 2019 ne wasu likitoci da suka kware wajen duba da masu tabuwar hankali suka koka da yadda kisan kai ke neman zama ruwan dare a Najeriya.
Bincike ya nuna cewa mutane 9.5 a cikin mutane 100,000 ne ke kashe kansu a Najeriya duk shekara. Sannan mutane 800,000 ne ke kashe kansu duk shekara a duniya.
Binciken ya kuma nuna cewa a kowani sakan 30 zuwa 40 akan samu wani ko wata na kokarin kashe kansan ko kanta sa a duniya.
Sannan kuma a watan Janairu 2017 ne wani likita mai suna Ibrahim Wakama ya sanar cewa sun koyo wasu ingantattun dabarun duba masu fama da matsalolin tabuwar hankali a kasashen Burundi da Rwanda.
Wakame yace wadannan dabaru kuwa zasu taimaka wajen warkar da mutanen da damu musamman ‘yan yankin arewa maso gabas da suka yi fama da Boko Haram.