Kungiyar masana kimiyar hada magunguna (PSN) ya koka da yawa-yawan ficewar ma’aikata masanana kimiyar hada magunguna daga kasar nan zuwa kasashen waje ya zama ruwan dare.
Shugaban kungiyar reshen jihar Oyo Abiodun Ajibade ya sanar da haka a taron wayar da kai game da wannan matsala da wannan kungiya ke fama da.
Ya ce wannan matsala na daya daga cikin matsalolin dake ci wa kungiyar tuwo a kwarya.
“Abin dake faruwa a kasar nan shine masana kimiyar hada magunguna da suka yi karatu a Najeriya na rawan jikin barin kasar zuwa kasashen waje musamman kasar Canada domin samun aikin yi da zaran sun kammala karatun su.
“Bincike ya nuna cewa daga cikin masana kimiyar hada magunguna 30,000 din da suka kammala karatunsu a kasar nan kuma suke aiki 5,000 sun fice zuwa kasashen waje sannan akwai wasu da dama da ke shirin kaucewa nan ba da dadewa ba.
“Hakan da da nasaba ne da rashin hadin kai tsakanin likitoci da masana magunguna a asibitocin gwamnati, rashin masana magunguna a asibitocin kudi da shagunan siyar da magunguna sannan da tsadan kudin magani da mutane ke fama da shi.
Ajibade ya ce babbar hanyar kawar da wannan matsala shine idan gwamnati ta hada kan duk ma’aikatan fannin kiwon lafiya domin inganta fannin a kasarnan.
“Kamata ya yi gwamnati ta kafa dokar da zai tilasta wa asibitocin kudi daukan masana magunguna a asibitocin su da shagunan saida magani.
Ya ce gwamnati za ta iya yin amfani da kimiya na yanar gizo domin taimaka wa mutane wajen samun shawarwarin da ya kamata kan irin magungunan da ya kamata su yi amfani da shi a lokacin da ake bukata.