Amfani da dabarun kayyade iyali ba su sa a kamu da cutar daji – Ma’aikatar Kiwon Lafiya

0

Shugaban sashen kula da kiwon lafiyar iyali na ma’aikatar kiwon lafiya Adebimpe Adebiyi ta bayyana cewa mace ba za ta kamu da cutar daji ba idan ta yi ko tana amfani da dabarun bada tazarar haihuwa.

Adebiyi ta ce sai an yi wa mace gwaji domin sanin dabarar da ya fi dacewa da jikinta kafin a bata maganin ta yi amfani da shi.

Ta ce fadin cewa ana kamuwa da cutar daji idan ana amfani da maganin kayyade iyali da kuma wai shan maganin na lalata mahaifar mace duk karya ne babu gaskiya a ciki.

Dalilin yin amfani da maganin kayyade iyali shine don ma’aurata su iya haihuwa a daidai lokacin da ya kamata sannan su haifi ‘ya’yan da za su iya tarbiyatarwa cikin koshin lafiya.

Adebiyi ta kuma yi kira ga mutane da su nisanta kansu daga sauraren khudubobin malaman addini da su kushe abin da hana wasu yin amfani da shi. Ta ce addinan da muke bi duk sun hadu akan yin amfani da maganin kayyade iyali bai saba wa karantar war addinan ba.

Shugaban sashen tsare- tsare da bincike na ma’aikatar kiwon lafiya Emmanuel Meribole ya ce gwamnati ta ware kudade domin inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana ta hanyar bada maganin kayyafe iyali a duk asibitocin gwamnati kyauta.

Meribole ya ce daga yanzu mata masu shekaru 15 zuwa 49 na da daman samun maganin babu fargaba.

Ya kuma ce gwamnati ta amince a ware wani kaso daga cikin kudaden inganta fannin kiwon lafiya wato ‘Basic Health Care Fund’ domin inganta kiwon lafiyar duk matasa a kasar nan.

Wadannan ma’aikatan kiwon lafiyar sun fadi haka ne a taron tattauna hanyoyin inganta kiwon lafiya a Najeriya da ake yi ranar Talata zuwa Laraba na makon jiya a Otel din ‘Nicon Luxury’ dake Abuja.

PREMIUM TIMES, PTCIJ, cibiyar PACFaH@Scale, gidauniyyar Pink Blue da kungiyar ‘Nigerian Governor’s Forum (NGHF) suka hada wannan taro mai taken ‘Samar da kiwon lafiya na gari ga kowa da kowa: Mahimmiyar rawan da gwamnati da masu fada a ji za su iya takawa domin inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan.

Matsalolin dake hana samun ci gaba a fannin kiwon lafiyar kasar nan da samar da hanyoyin da suka fi dacewa domin ganin talakan Najeriya ya samu kiwon lafiya nagari sannan cikin farashi mai sauki na daga cikin batutuwan da ake tattauna a taron.

Share.

game da Author