Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana cewa akwai matasa masu ilmi, amma nakasassu har 81 da ta dauka domin aikin zaben gwamna a Jihar Kogi.
Za a gudanar da zaben gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa a ranakun 16 Ga Nuwamba.
Daraktan wayar da kai dangane da al’amurran zabe na jihar Kogi, Ahmed Biambo ne ya bayyana haka a jiya Laraba, a wurin wani taron wayar dan masu nakasa da za su gudanar da aikin zabe a jihar ta Kogi.
Biambo ya shaida wa manema labarai cewa wadannan nakasassu 81 an dauke su ne a matsayin jami’an zabe da mataimakan jami’an zabe.
Daga nan sai ya ce duk za a tura su a jihohi 21 na jihar, amma ba za a tura su a yankunan da ake zaman dar-dar din kaffa-kaffa da barkewar rikici ba.
Biambo ya ce Kwamishinan Zabe na Tarayya a Jihar Kogi (REC), ya umarce su da a tura nakasassun a yankunan da ba a tunanin wata tashin-tashina.
Shi kuwa Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Nakasassu ta Kasa (JONAPWD), Solomon Yahaya, ya tabbatar da daukar nakasassun aikin zaben a Jihar Kogi ga PREMIUM TIMES.
Ya gode wa INEC dangane da kaifin tunanin da ta yi wajen daukar nakasassun yin aikin zabe. Hakan inji shi ya kara tabbatar wa nakasassun cewa a ba maida su saniyar-ware ba.
Sannan ya yi kira ga dukkan nakasassun da aka dauka aikin zaben su yi aiki tsakanin su Allah tare da kishi ba tare da son kai ba.
Can a Jihar Bayelsa kuma, inda za a gudanar da zaben gwamna a rana daya da Kogi, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta yi kakkausan gargadin cewa Dimokradiyya ba kayan sayarwa ba ce. Don haka duk mai kokarin sayen kuri’u a loakcin zaben gwamna, to ya kuka da kan sa.
Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya yi wannan dangane da gabatowar zaben gwamna a Jihar Bayelsa.
Yakubu ya yi wannan gargadi a lokacin da ya ke taron ganawa da sarakunan gargajiya na Jihar Bayelsa, inda ya fassara sayen kuri’u tamkar cefanar da dimokradiyyar Najeriya ce a kasuwar ‘yan gwan-gwan.
A taron wanda aka gudanar a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa, Yakubu ya ce sayen kuri’u na daya daga cikin kalubalen da INEC ke fama da shi a lokutan zabe a kasar nan.
“Damuwar mu ta farko ita ce kalaman da ka iya haddasa barkewar rikici a lokutan kamfen, lokutan gudanar da zabe da kuma lokutan da ake tattara sakamakon zabe.
“Wani kalubalen kuwa shi ne saye da sayar da kuri’u. Bai yiwuwa a bar wasu ‘yan gwan-gwan masu kokarin saida dimokradiyya a tsakiyar kasuwa; ya zama tilas a bar kowane dan Najeriya ya zabi wanda ya ke ra’ayi a ranar zabe, ba tare da an cunna masa kudi ya saida ‘yancin sa ba.
“Ya kamata mu tashi tsaye mu dakile annobar sayen kuri’u. INEC ba jam’iyyar siyasa ba ce, kuma ba ta goyon bayan kowace jam’iyya, ko wani dan takara. Wanda jama’a suka zaba, shi ne zai wakilce su.”