2017 ZUWA 2019: Boko Haram sun kashe sojoji 2006

0

Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ke ta yawan nanata cewa yanzu Boko Haram sun zama gurgun-mage, ba su iya wani tasiri, sai dai kai hare-hare inda ke da karancin tsaro, wani bincike ya nuna cewa a cikin shekaru uku Boko Haram sun kashe sojoji 2006.

Rahoton wanda SBM Intelligence ta fitar cikin makon da ya gabata, sun tattara su ne daga labaran da PREMIUM TIMES da wasu jaridu suka rika bugawa dangane da sojojin da suka rasa rayukan su da kuma wadanda aka jikkata.

Yayin da Shugaba Buhari ke yawan furta cewa Boko Haram ba su iya wani katabus, sai dai kai hare-hare a yankunan da ke da karancin tsaro, labaran da PREMIUM TIMES ta rika bugawa sun tabbatar da cewa Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare har cikin sansanoni da Brigade-brigade na soja har wuri uku, inda aka kashe sojoji da dama tun daga cikin watan Yuni, 2018.

Nanatau

Tun cikin shekarar 2015 Shugaba Muhammadu Buhari ke ta nanata cewa an gama da Boko Haram, sai dai ’yan burbushin su masu kai hare-haren sunkuru a yankunan da babu isasshen tsaro, “soft targets”, kamar yadda ya ke ta yawan furtawa.
Yayin wannan jawabi a lokacin da Hukumar Tsaron Sojoji ta sake kaddamar da shirin karasa murkushe Boko Haram, bayan da Buhari ya hau mulki cikin 2015.

Rahoton ya nuna yadda aka kashe sojoji birjik a cikin 2016, shekarar da Buhari ya fara shafewa dindi a matsayin shugaban kasa.

Sai dai kuma rahoton da SBM Intelligence, kungiya mai bin diddigi da kadin al’amurran tsaro, siyasa da tattalin arziki ta fitar, ta ce akalla tun daga lokacin da Buhari ya yi wancan furuci zuwa makon da ya gabata, an kashe sojoji 2,482.

Adadin da SBM Intelligence ta fitar daga 2011, ya nuna cewa shekarar 2014 ce aka fi kashe sojoji da yawa, har 2,789 a yakin Boko Haram. Adadin ya ragu sosai bayan da Buhari ya hau mulki, zuwa sojoji 189 kacal cikin 2015.

Sai dai kuma adadin wadanda suka rasa rayukan na su ya ci gaba da yin yawa cikin 2016, inda aka kashe sojoji 387, sai kuma sojoji 472 cikin 2017, sai kuma aka kashe sojoji 661 cikin 2018. A cikin 2019 kuma an kashe 873 ya zuwa ranar 12 Ga Satumba.

Wannan na nuni da cewa watakila adadin wadanda aka kashe din kan iya canjawa a cikin 2019, domin babu kididdigar wadanda aka kashe daga ranar 13 Ga Satumba, zuwa karshen 2019 nan da watanni kusan uku kenan.

JADAWALIN SOJOJIN DA BOKO HARAM SUKA KASHE A KOWACE SHEKARA DAGA 2011 ZUWA 2019

2011 85
2012 229
2013 71
2014 2789
2015 189
2016 287
2017 472
2018 661
2019 873

2011 ZUWA 2019: AN KASHE SOJOJI 5,656

Jimillar adadin sojojin da SBM Intelligence ta ce an kashe tsakanin 2011 zuwa 2019 sun kai 5.656 tun fara yakin Boko Haram. Sai dai kuma kididdigar ba ta bayar da bayanin wadanda suka rayukan su cikin 2010 da 2009, lokacin da guguwar Boko Haram ta fara tirnikewa.

BABU RAHOTON TAKAMAIMEN ADADI DAGA BANGAREN SOJOJI

Babban manazarcin SBM Intelligence, Cheta Nwanze, ya ce adadin da suka tattara zai iya canjawa, domin bangaren sojoji ba su bayar da sahihin rahoto, domin ba a san makomar wasu sojojin ba, musamman wadanda suka bace a lokacin yaki, har yau ba a kara jin duriyar su ba.

SMB ta danganta yawaitar adadin wadanda suka rayukan su cikin 2016 da fandarewar da Abu Musab al-Barnawi ya yi daga bangaren Shekau, ya ja rundunar sa ya samu kawance daga ‘yan ta’addar ISWAP.

RAGUWAR JEFA BAMA-BAMAI, RUGUZA MASALLATAI, COCI DA KASUWANNI

A daidai lokacin da ake samun karuwar kisan sojoji sosai, hare-haren bama-bamai a cikin jama’a farar hula, wuraren ibadu, unguwanni da kasuwanni ya ragu matuka kwarai.

Rahoton SBM Intelligence ya ce an samu wannan raguwar kashe fararen hula ne saboda bangaren Al-Barnawi ya maida hankali wajen kai wa sojoji hari, maimakon fararen hula.

Manazarta da masu sharhi da dama sun ki yarda da ikirarin da Buhari ke yi cewa an gama da Boko Haram, sai burbushin masu kai ‘yan hare-hare kawai.

Share.

game da Author