Ilmantar da ‘ya’ya mata ne kadai zai magance yawan al’umma -Sarkin Kano

0

Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana cewa sai an ilmantar da ‘ya’ya mata kuma an dauke su da daraja sannan matsalolin kasar nan za su fara raguwa.

Sarki Muhammadu Sanusi ya yi wannan magana a wurin taron Makomar Tattalin Arziki na 2025 da ke gudana a Abuja, a jiya Litinin.

Ya fito a matsayin shugaban kwamitin tattauna wata makala, mai suna 2050: Yawan Arziki Ko Taron Yuyuyu?

A cikin kwamitin har da Gwamnan Jihar Ekiti, kuma Shugaban Gwanonin Arewa, Kayode Fayemi, Mathew Hassan Kukah da kuma Shugabar Kamfanin Jumi’a, Juliet Anammah.

Sarkin Kano ya ce duk wata matsalar da ta dabaibaye kasar nan, Boko Haram, garkuwa da mutane, rikicin Fulani da makiyaya, matsalar yara da su makaranta, duk yawan al’umma barkatai ne ya haifar da su.

“Za a ga fa’ida idan aka dauki mace a matsayin dan Adam kamar yadda ake kallon namiji. Ta samu hakkin ilmi, kudaden shiga, da sauran su, yadda ita ma za ta gina da gyara rayuwar jama’a.

” Amma an wayi gari kawai ana yi wa mata kallon wata masana’antar haihuwar jarirai. Su ma jariran idan sun girma a maida matan cikin su masana’antar haihuwar wasu jariran, to akwai matsala.”

Sarki ya ce a lokacin da ya nemi bijiro da wayar wa mata kai da ilmantar da su a Kano, malamai sun yi masa caa, ana cewa wai zai shigo da tsarin hana haihuwa.

Sai dai kuma ya kwankwashi kan gwamnati, inda ya ce ta daina sukar yaran da na su zuwa makaranta, saboda ba ta wadata jama’a da makarantu da malamai ba.

Ana ci gaba da nuna damuwa cewa nan da 2050, yawan ‘yan Najeriya zai iya kai milyan 400.

Share.

game da Author