Tsoron EFCC ya sa gwamnoni sun daina shirya dabdala, bushasha da ragabza -Magu

0

Shugaban Riko na EFCC, Ibrahim Magu, ya bayyana cewa tsoron idanun EFCC ya sa gwamnonin kasar nan sun daina shirya dina da walimar ragabza, dabdala da kuma bushashar kashe kudade.

Magu ya yi wanann furuci ne a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai, yayin ziyarar da yaki Ofishin Shiyya na EFCC da ke Makurdi.

Ya ce a yanzu duk inda mutum wani mai rike da mukami zai shiga a kasar nan, to idanun EFCC Na wurin. Shi ya sa gwamnoni da sama sun daina shirya bushashar ragargazar kudade.

“Duk inda za su shiga to akwai idanun EFCC, za ta sa ido. Da ta ga an yi abin da ya kauce da kudade, to za ta dira ta yi aikin ta. Ko a nan Najeriya, ko a kasashen waje.

Magu ya ce duk da irin tarnaki da dabaibayi da kalubalen da ake fuskanta a kan yaki da rashawa da cin hanci ana samun nasara sosai.

“Kullum mabarnata sai shigo da hanyoyi da sabbin dabarun zamba da kauce wa hukuma su ke yi. Musamman hanyoyin sadarwar zamani. To amma kuma ba su sani ba, tuni EFCC ta yi nisa wajen kwance duk wani kulli da za su yi.” Inji Magu.

Ya kuma sha alwashin ci gaba da aikin sa ya na dakile cin hanci, rashawa da zambar kudade. Magu ya bayyana nasarar da EFCC ta samu wajen kokarin dakile matasa ‘yan Yahoo Yahoo.

A karshe ya bayyana cewa kwanan baya EFCC ta kwato wasu makudan kudade a Majalisar Jihar Taraba.

Share.

game da Author