Dalibai 12 za su maimaita bautar kasa a jihar Neja

0

Kodinatan hukumar (NYSC) dake jihar Neja Funmilayo Ajayi ta bayyana cewa dalibai masu bautan kasa na rukunin zubin 12 za su maimaita bautar kasar su a jihar.

Ajayi ta sanar da haka ne da take ganawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Minna ranar Talata.

Ta ce wadannan masu bautan kasan za su maimaita shekara daya ne saboda gujewa wuraren da aka tura su yin bautan kasa ba tare da sun nemi izini ba da suka yi.

Ajayi ta ce a wannan shekara hukumar NYSC ta karrama masu bautan kasa shida saboda gagarimar gudunmawar da suka bada a lokacin da suke bautan kasar su a jihar.

An yi kira ga duk wadanda suka kammala bautan da su yi amfani da dabarun sana’ar hannu da suka koya a kokacin da suke bautan kasan domin cin gashin kansu.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne masu bautan kasa 26 suka maimaita bautar kasar su a jihar Kano.

Wadannan masu bautan kasa 26 za su kammala bautan kasar su ne tsakain wata daya zuwa hudu a jihar.

Share.

game da Author